Ƙungiyar Mawaƙan Sabon Rai ta Cocin Ikilisiya sun karrama tsofaffin shugabanin ta

Daga RABI’U SANUSI

A ranar Lahadi ne ƙungiyar kai bushara ta mawaƙan sabon rai da ke cocin Ikilisiyar Angilican ta Ƙaramar Hukumar Fagge cikin Jihar Kano ta karrama tsofaffin shugabanin ta da sukai aiki tuƙuru da cigaban yaɗa addini Kiristanci.

Kamar yadda tsohon ɗan takarar majalisar jiha na Ƙaramar Hukumar Rogo, kuma mai tsawatarwa a wannan ƙungiya, Hon Haruna Yahaya Kadana ya yi ma manema labarai ƙarin haske jim kaɗan bayan kammala taron karramawar bayan gudanar da addu’o’i kamar yadda aka saba a duk ranakun Lahadin mako.

Haruna Kadana ya ce, bai taɓa tunanin zai zama ɗaya daga cikin waɗanda za a karrama ba a wannan rana, amma sai ga shi sunansa ya fito cikin zaƙaƙuran mutanen da aka karma a wannan Ikilisiya ta Angilican da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.

Tsohon ɗan takarar ya ƙara da cewa, zai yi amfani da wannan dama domin kira ga shugabanin da aka zaɓa da babbar murya da cewa, ya kamata su waiwayi talakawan da suka zave su dan rage masu raɗaɗin rayuwa da aka samu kai a halin yanzu.

“Ni na sani idan za mu rinƙa shiga cikin mutanenmu to lallai babu abinda zai sa ba za mu fahimci halin da suke ciki tare da taimaka masu da abin da Allah ya bamu dama ba,” inji shi.

Hon Rogo Kuma ƙara da cewa, yazuwa yanzu a shirye yake wajen ganin an taimaka wa al’umma kama daga Musulmai da Kiristoci dan cigaba da samun haɗin kai da zaman lafiya a tsakin al’umma da ƙaunar juna.

Shima wakilin shugaban Cocin na Ikilisiyar Angilican ta Fagge, Mista Joshua Kubai, ya bayyana cewa, wannan ƙoƙari na mawaqan na sabon rai abin a yaba ne, musamman yadda sukai tunanin karrama tsofaffin shugabanin da suka gada dan aikin bushara.

Mista Kubai ya qara da cewa, aikin bushara na da buƙatar matasa kamar waɗannan don isar da saƙon Yesu Almasiyyu zuwa lungu da saƙo a wannan lokaci.

Daga ƙarshe ya lurar da mutane kan abinda aka fi buƙata a aiki irin wannan na bushara, inda ya ce, a wannan aiki na bushara abinda aka fi buƙata shi ne, isar da saƙo dan wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *