Ƙungiyar Mercy ta kashe sama da milliyan ɗaya wajen fitar da fursunoni a Kebbi

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi

Wata ƙungiyar mai suna Mercy Organization ƙarƙashin jagorancin Honarabul Bashar Aliyu, da ke da cibiya a Jihar Kebbi ta fitar da fursunoni da dama a jihar da ke zaman kurkuku sanadiyyar bashi da makamantansa.

Honarabul Bashar Aliyu mataimaki ga ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki kuma ɗaya daga cikin shugabannin ungiyar ya bayyana wa wakilinmu cewa ya zama wajibi ga duk wanda ke da halin taimaka wa al’umma ya taimaka ta inda duk zai iya.

Ya ce, ya kashe sama da naira milliyan ɗaya wajen ganin ya fitar da waɗansu fursunoni goma sha biyar musamman waɗanda ba shi da bai taka kara ya karya ba ne sanadiyyar zuwan su gidan gyaran hali.

Hakazalika, ya ƙara da cewa an bai wa waɗanda suka sauke Alƙur’ani maigirma buhun shinkafa da dubu ɗari don taya su walimar sauka da za a gudanar.

Ya ƙara da cewa, tallafa wa irin waɗannan mutanen yana ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ganin sun zama mutanen kirki bayan kammala zamansu a gidan gyaran hali.

Da ya ke jawabi shugaban ma’aikatan gidan gyaran hali na Birnin Kebbi ya yaba wa wannan ƙungiyar bisa ga irin wannan ƙoƙarin na kulawa da mutanen da ke ajiye a gidan gyaran hali.

Ya bayyana cewa wannan hukumar tana koyar da karatu da sana’o’i inda yanzu haka akwai mutane da yawa da suka koyi sana’o’i da suka tsaya da kafafuwansu bayan kammala wa’adin zamansu a wannan gidan.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan ƙungiyar saboda bayan sakamakon da mutum zai samu a lahira tun daga nan duniya Allah zai faranta masa rayuwarsu.

Bayan wannan kuma yana taimakawa wajen rage cinkoso da ke haifarda rashin lafiya daban-daban musamman waɗanda ake ɗauka daga ɗan Adam zuwa wani mutum.