Ƙungiyar Miga Ina Mafita ta yi zargin samun cushen ma’aikatan lafiya a Miga

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Wata ƙungiya mai rajin cigaban ƙaramar Hukumar Miga wato Miga development Association wadda akafi sani da ‘Miga Ina Mafita’ ta gabatar da takardar ƙorafinta ga manema labarai tana neman Gwamnatin Jihar Jigawa ta taimaka ta shawo kan matsalar da suke ciki wajen daƙile damar da ’ya’yansu ke da ita wajan ɗaukar ma’aikatan lafiya da gwamnatin jihar ta bada damar a ɗauka.

Shugaban ƙungiyar ta Miga Ina Mafita, Malam Abubakar Ahmed shi ne ya sanya wa takardar hannu.

Ya ƙara da cewa, yaransu 14 aka ƙi ɗauka aikin kiwon lafiya a lokacin da suka tura sunayansu ma’aikatar lafiya kuma aka yi masu cushen yara 9 wazanda ba su da wata alaƙa da ƙaramar Hukumar ta Miga a matsayin ’yan asalin ƙaramar Hukumar ta Miga.

Ya ci gaba da cewa, hasalima an sami mutun uku daga cikinsu ba su da wata takardar shaidar karatun kiwon lafiya amma an cusa sunayansu a matsayin ‘yan asalin yankin a matsayin ma’aikatan lafiya da za su yi aiki a ƙaramar Hukumar ta Miga.

Bayanin da ya ke yi ya nuna cewa wasu daga cikin yaran da aka yi wa ƙaramar Hukumar Miga cushen da su ‘yan asalin ƙaramar Hukumar Jahun ne da ƙaramar Hukumar Taura, ba su da wata alaƙa da Miga.

Ya ci gabada cewa, daga cikin waɗanda aka ba da sunayan na su akwai Hannatu shehu Jahun, Rabiatu Sani Musa Jahun, Shafiatu Abubakar Jahun, Saratu Abdulmutalib Taura.

Sauran su ne Saminu Muhd Jahun da Umar Abdu Jahun sai kuma wasu yara uku da bincike ya nuna su ba su ma da wata takardar shaidar karatun aikin lafiya da suma aka cusa sunayansu a cikin jerin sunayan ‘yan asalin aaramar hukumar ta Miga, waɗanda tuni aka turasu cibiyoyin kiwan lafiya na yankin a matsayin sabbin ma’aikatan lafiya domin su kama aiki.

Saboda haka ne suke neman Mai Girma Gwamna Umar Namadi ya sanya idanu kuma ya yi bincike Akan al’amarin domin ba a yi masu adalci ba wajan ɗaukar ma’aikatan lafiyar kamar yadda gwamna ya bada umarnin a ɗauki ‘yan asalin ko wanne yankin.