Ƙungiyar NANS ta yi Alla-wadai da ra’ayin shawartar Jihohi kan mafi ƙarancin albashi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa, wato NANS ta yi Alla-wadai da kiran da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya yi kan tattaunawa da jihohi game da batun mafi ƙarancin albashi.

Kayode ya yi wannan kira ne a makon da ya gabata inda yake cewa yana ganin dacewar kowace Jiha ta tattauna da wakilan ƙungiyoyin ƙwado kan abun da zata iya biya na mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatanta.

A wata sanarwa da akawon ƙungiyar, Abdul-Yakinn Odunayo ya fitar a ranar Litinin, ya ce wannan wani mataki ne na ƙin ma’aikatan da alheri ga tsohon gwamnan.

Mafi ƙarancin albashi abu ne da gwamnatin tarayya da hukumomin ƙwadago ke tattaunawa tsawon watanni inda gwamnatin ta ce zata ke biyan 62,000 yayin da ƙungiyar ƙwadago ta kafe a kan naira 250,000.

Fayemi ya yi furucin ne la’akari da banbance-banbancen kuɗin shiga da kuma arziƙin kowace Jiha inda NANS ta ƙi amincewa da hakan tare da kira ga gwamnati da ta yi watsi da shawararsa gami da tabbatar da buƙatar ƙungiyar ƙwadago domin jindaɗi da walwalan ma’aikata.