Ƙungiyar ‘Neighborhood Development Associantion’ ta gudanar da ayyukan cigaban al’umma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A cigaba da gudanar da muradun da suka assata, Ƙungiyar ‘Kwanar Bushara Neighborhood Development Associantion’ da ke Unguwar Rigasa ta Jihar Kaduna ta gudanar ayyukan gyaran tituna domin jin daɗin jama’a.

Ƙungiyar ta kwashe makonni biyu tana fitowa duk ranar Lahadi domin cike ramukan da suka addabi direbobi da sauran jama’a a kan babban titin Maƙarfi Road, inda suka rinƙa bi suna cike manyan ramuka da ƙanana.

Wakilinmu da ya shaidi wannan aiki ya shaida mana cewa, mambobin ƙungiyar sanye da rigunan da ake alamta su ne suka rinƙa bi suna haƙewa tare da cike ramukan da kwaɓaɓɓen siminti, yashi da duwatsu.

Wannan aiki an gudanar da shi ne tun daga babban titin bypass har zuwa Kwanar Bishara, wanda a wannan tsakanin ne titin ya fi lalacewa.

Cikin zantawarsa da wakilinmu, Shugaban wannan ƙungiya, Malam Muhammad Garba Lado ya bayyana cewa suna gudanar da waɗannan ayyuka ne bisa taimakon da suke samu daga mambobin wannan ƙungiya, masu taro-sisi da kuma kayan aiki.

Ya ci gaba da qarin haske da cewa, “a wannan aiki da muka gudanar na gyaran titin Maqarfi Road, baya ga taimakon jiki da na dukiya daga mambobin mu, mun samu taimako daga ƙungiyar direbobin motocin ‘yar ƙumbula (mini bus), waɗanda kusan duk da su ne muka gudanar da wannan aiki.”

Shugaban ƙungiyar ya ci gaba da bayyana cewa, “ko a lokacin gudanar da aikin, in ka duba za ka ganmu da rigunan mu na Neighborhood, sannan kuma abokan aikin namu na Union ɗin ‘yar qumbula su ma suna sanye rigunansu, hatta shugaban su ma yana cikin aikin nan. “

Malam Lado ya ci gaba da bayyana cewa baya ga gyaran wannan hanya, a shekarun baya ma sun gudanar da irin wannan aiki a babbar hanyar da ta haɗa Unguwar Rigasa da Nariya, wacce ya ce babbar hanya ce, amma saboda rashin kyawunta har nema ta ke yi ta gagara bi, musamman da damina.

Sai dai shugaban ya bayyana cewa, bisa naci da yawan rubuce-rubucen neman taimakon hukuma da ƙungiya ta yi ta rubutawa, yanzu haka gwamnatin jihar Kaduna ta bayar aikin hanyar, wanda za a haɗe Rigasa, Nariya da Kabala.

“Muna miqa matuƙar godiyar mu ga mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad el-Rufai bisa aikin wannan hanya da ya bayar sakamakon yawan koken da muke yi masa. Muna godiya, tare da yin addu’ar Allah ya sa a kammala wannan aiki cikin nasara,’ in ji shi.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ba a aikin gyaran hanya kawai suka tsaya ba, “domin mun kai agaji zuwa ƙaramin asibitin da ke wannan yanki namu a Miyetti-Allah, inda muka gina masu ɗakin mai gadi, feshin maganin ciyawa da sauransu,” ya ce.

Ya ci gaba cewa sun kuma taimaka wa jami’an tsaro na KADVIS da Cociloli domin su samu gudanar da ayyukan su cikin nasara.

“Haka kuma, bisa taimako da muka samu daga mambobin mu, a cikin azumin da ya gabata, mun raba wa mabuƙata kayan salla, musamman marayu, inda muka raba masu suturori, kuɗaɗe da kayan abinci. Muna fata kuma, in Allah ya yarda za mu rinqa gudanar da waɗannan ayyuka duk shekara, ko kuma lokaci zuwa lokacin,” in ji shi.

Da yake qarin haske game da waɗannan ayyuka da ƙungiyar ke gudanarwa, Sakataren wannan ƙungiya, Malam Aliyu Saleh Muhammad, ya bayyana cewa dama dai maƙasudin kafa wannan ƙungiya tasu shi ne taimaka wa al’umma ta fannoni da dama.

Malam Aliyu ya ce, ko gyaran hanya da suka gudanar na titin Maƙarf Road, ba wai direbobi ne kaɗai ke jin daɗin bin hanyar ba, hatta fasinjoji ma gyaran yana masu daɗi. Sannan ya ce “aikin gyaran hanyar Nariya da Chairman ya yi maku bayani, kafin mu yi gyaran, hanyar neman gagara bi ta yi,” ya ce.