Ƙungiyar PHRC ta shirya wa jami’an tsoro na sa-kai bita

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Ƙungiyar wanzar da zaman lafiya, tsaro da kare haƙƙin ɗan adam (PHRC) ƙarƙashin shugabancin Idris Ɗahiru Ofisa ta shirya wa Jami’an tsaron sa kai bitar sanin makamar aiki kan yadda za a tsaftace aikin gudunmawarsu ta ba jama’a da ƙasa tsaron don zaman lafiya ƙasa kamar yadda ya kamata a yi aikin bada tsaron farin kaya na sa kai.

Taron wanda aka gabatar a unguwar bamfai Kano a ranar Asabar ɗin da ta gabata ya sa mu halatar jami’an tsoro na ’yan sanda da lauyoyi da sauran masana domin ilimantar da jami’an tsaron sa kai kamar ’yan bijilanti da ’yan agaji da ’yan karota da dai sauransu a wannan bita ta yini gudu wanda aka yi a Kano.

A jawabinsa, mataimakin kwamishinan ’yan sanda na ɓangaran tsare-tsare na Kano, AC Abubakar Abdullahi Shika, ya yaba wa shugaban ƙungiyar kan irin wannan aiki na su na taimaka wa harkar tsaro da irin waɗanan ƙungiyoyi sai kai ki yi ako da yau shi a wanan zamani da ake da buƙatar haka inda kuma ya bayyana Kano a matsayin jiha da ke kanga ba wajan zaman lafiya a Nijiriya bisa taimokon Allah da kuma yadda shugaban ’yan sanda, na ƙasa da kwamishinan ’yan sanda na Kano da gwamnan Ganduje suka tsaya tsayin daka wajen aikin samar da tsaro a Kano.

Haka kuma akwai Lauya Barista Aliyu da Lauya Barrista Kamalu Yahaya wanda suka gabatar da takardu kan yadda jami’an tsaron farin kaya za su yi aiki daidai da matsayin ƙasar.

Dakta Kwamare Yahaya Ɗanjuma Yusuf wanda shi ne uban ƙungiyar na ƙasa ya bayyana irin waɗanan ƙungiyoyi a matsayin abokan cigaban jiha da ƙasa baki ɗaya.

Inda shugaban PHCES Ɗahiru Idris Ofisa ya nuna gamsuwa kan irin haɗin kai da suke samo daga ’yan sanda da sauran jami’an tsaro inda kuma ya buƙaci sauran Jami’an tsoron farin kaya irinsu Hisba da Karota da sauransu kan su riƙa tura jami’ansu bita akai-akai don samun gogewa da iya horar da jama’a akan aikinsu na gudunmawa tsaron ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *