Ƙungiyar Raya Garin Tafawa Ɓalewa ta gindaya wa Sayawa sharuɗɗan samun masarauta

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

An gindaya wa al’ummar Sayawa dake cikin ƙananan hukumomin Tafawa Ɓalewa da Bogoro na Jihar Bauchi sharuɗɗa na cimma buƙatar su ta samun masarauta da ‘yancin cin gashin kai kamar yadda hukumar Shari’a ta Alƙali Babalakin ta shawarta dangane rikicin ƙabilanci da ya faru a garin Tafawa Ɓalewa a ranar Litinin 22 ga watan Afrilu na shekara ta 1991.

Ƙungiyar raya garin Tafawa Ɓalewa wacce ta zayyana waɗannan sharuɗɗa, ta kuma fayyace su ɗaya bayan ɗaya da suka haɗa da bin ƙa’idoji kamar yadda shuɗaɗɗiyar gwamnatin Isa Yuguda ta yi a shekara ta 2011.

Ƙungiyar raya garin na Tafawa Ɓalewa ta ƙara da cewar, “Ba za a kamfaci ƙasar wata al’umma ba domin sanya ta cikin masarautar da za a ƙirƙiro ba tare da izinin su ba, kamar yadda wajibi ne a shawarci duk wata al’umma walau tana son kasancewa cikin masarautar da za a ƙirƙiro ko za ta cigaba da zama cikin masarautar Bauchi.

Ƙungiyar, a cikin wata takardar jawabi a ranar Talata da ta gabata ta kuma gindaya sharaɗin ba za a kashe rayuka ko halaka dukiyoyin jama’a ba, kamar yadda ya faru a shekarun 1991, 1995, 2001, da 2011 lokacin da aka hallaka rayukan mutane da basu kina balle gani, haɗu lalata dukiyoyin jama’a na miliyoyin nairori.

Jawaban cikin takardar sanarwar wacce shugaba da sakataren ƙungiyar, Shu’aibu Salej Umar da Yunusa Ado suka sanya hannuwa, sun fadi ƙarara ba sau ɗaya ko biyu ba cewar, basu gudun a baiwa Sayawa masarautar ta kansu.

Idan za a iya tunawa dai, hukumar binciken aukuwar rikicin Tafawa Ɓalewa na shekara ta 1991 a yayin gudanar da aikin da aka ɗora mata, ta gano tare da zayyana sunayen waɗanda take zargin akwai hannuwan su cikin tayar da rikicin, tare da bayar da shawara na ƙara bincike akan su, haɗu da gurfanar dasu a gaban shari’a.

Shugaba da Sakataren ƙungiyar sun yi matuƙar jin takaici yadda gwamnatocin jihar Bauchi da suka shuɗe basu shawarar zurfafa bincike da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kuliya ba, lamarin dake nuni da cewar, Sayawa zasu iya aikata kowace irin ta’asa, kuma su sha babu wata fargaba.

“Gwamnatoci da suka shuɗe basu aikata abinda ya kamata ba na cafke waɗanda aka samu da hannuwa a cikin rikicin, tare da gurfanar dasu gaban kuliya biyo bayan mummunar rawa da suka taka a mafi munin rikici na shekara ta 1991 da aka zubar da jinin talakawa waɗanda ba su jiba, ba su gani ba.

“Waɗansu shugabannin masu laifukan tayar da rikicin suka fara bayyana daga bisani. Ɗaya daga cikin su shine Kwamandan Mayaƙa sama Ishaku Komo mai ritaya, wanda ya bugi ƙirjin aiyana kansa a matsayin Basarake da zai jagoranci masarautar ta Sayawa da za a ƙirƙiro nan gaba. Ba shi kaɗai bane, yana Ubannin gida da masu giya masu baya”, kamar yadda ƙungiyar ta gano.

Shugaban ƙungiya Shu’aibu Umar ya bayyana cewar, gwamnatin jihar Bauchi mai cice ta bayar da umarnin a cafke wanda ya ayyana kansa a matsayin sarkin na Sayarwa, kuma a halin yanzu yana shan tuhumce-tuhumce na kotun Shari’a, wanda Umar yace ɗaukar wannan mataki yayi daidai.

Shugaba Umar ya kuma lura da cewar, wannan mataki da gwamnati ta ɗauka wani nuni ne na ƙarfin halin yin hukunci ga duk wani mai kaifin tayar da hankalin jama’a, yana mai faɗin, babu wani mahaluki da zai nuna isa a daura da shugabanci nagari.

Umar ya yi kuma tuni da cewar, an gabatar da wani ƙudurin doka wanda majalisar dokokin jiha ta amince kuma Gwamna ya rattaba hannu na ƙirƙiro masarautar Sayawa a shekara ta 2011 wacce za a wa shalkwata a garin Bogoro, wanda abin takaici Sayawa suka bujewa, suna mai da’awar shalkwatar masarautar ta kasance a garin Tafawa Ɓalewa.

“Duk da cewar, dukkan takardun tarihi, shaidu da sassalar yare sun yi nuni da cewa garin Tafawa Ɓalewa Fulani ne suka kafa ta, Dayawa basu da wannan masaniya. Saboda da haka kenan Sayawa suke gurgunta wannan bukata tasu na samun masarautar ta hanyar kaiwa ƙararraki zuwa kotuna, a ciki da wajen jihar Bauchi.”

Ƙungiyar ta raya garin Tafawa Ɓalewa sai ta jaddada aniyar Gwamnatin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed na kawar da duk wata shegantaka da rashin bin doka da raini wa hukumomin gwamnati daga kowane ɓangare ne na al’ummar jihar Bauchi.

Kamar yadda ƙungiyar tace, Gwamna Bala Mohammed ya ɗaura aniyar sanya ƙafar wando da duk wasu gungun jama’a masu don tayar da zaune tsaye, masu tutiyar kawo tashin hankali, komai matsayinsu, addini ko yaren su a cikin ɗaukacin al’umma da a ko yaushe suke da’awar zaman lafiya da cigaban jihar Bauchi.

Alh. Shu’aibu Umar saboda da haka ya jinjina wa Gwamna Bala Mohammed bisa jaruntakar sa ma ɗaukar waɗannan matakai da gwamnatocin baya tun shekarar 1991suka kasa zaƙulo masu laifukan wancan rikici da wanda ya aiyana kan sa a matsayin Sarkin Sayawa ke jagoranci da sunan Sarki Gung Zaar, da shugabannin sa waɗanda suka yi bultu da kuma waɗanda suke yi masa tura mai kantu ruwa.