Ƙungiyar Rayuwar Mata ta tallafa wa mutum dubu 20 da abinci a Nijar da Nijeriya

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato

Kowacce shekara ƙungiyar Rayuwar Mata, da ke tallafawa cigaban mata, wacce Malama Khadija Abubakar ke jagoranci, tana raba wa mabuƙata abincin buɗe-baki, a lokacin azumin Ramadan, kamar yadda take gudanarwa a wannan shekarar.

Kawo yanzu ƙungiyar ta baba abinci ga jama’a da dama da suka haɗa da ’yan gudun Hijira, waɗanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su, akwai masu lalura ta musamman, akwai zawarawa, uwayen marayu, da almajirrai da sauransu. An tsara gudanar da aikin rabon abincin a wasu sassan garin Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, da wasu yankuna na jihohin Zamfara, Sakkwato, Katsina a Nijeriya.

Gwamnan Jihar Maraɗi wanda ya samu wakilcin shugabar Hukumar Tallafawa ‘Yangudun Hijira ta ta Jihar Maraɗi, Madame Fatouma Soumana, shi ne ya jagoranci ƙaddamar da fara rabon abincin, ya aika da saƙon yabo da jinjina ga wannan ƙungiya, sakamakon irin tallafin da take bayarwa, yana mai cewa wannan abincin sadaka da ake bayarwa ya zo a lokacin da ake buƙata.

A nata jawabin shugabar ƙungiyar Rayuwar Mata, Hajiya Khadeeja Abubakar ta bayyana cewa, a bana ma sun samu tallafin ne daga Gidauniyar Zakka ta wasu bayin Allah da ke Amurka, waɗanda suka ɗauki nauyin raba shinkafa, man gyaɗa da suga ga iyalai sama da dubu 15. Yayin da ta ƙara da cewa, ana sa ran mutum dubu 20 ne za su amfana daga rabon abincin buɗe-baki.

Ta ce, a kowacce rana za a riƙa raba abincin mutum sama da 500, har zuwa ƙarshen azumi. Wanda ake baiwa Mutun sama da Dari biyar, kulli yaumin har azumi ya kare da ake Rabawa wurare daban daban.

Shugaban ‘Yangudun Hijira na ɓangaren Nijeriya Malam Sallau Abdullahi, daga garin Kaka a yankin Tsibirin Runji, ya yi godiya ga ƙungiyar Rayuwar Mata da Gidauniyar Zakka da suka raba sadakar abinci, tare da yabawa Gwamnatin Jihar Maraɗi kan samar masu da muhallin da suke zaune. Ya ce sun share kusan shekara biyar a wajen da suke zaune, inda yawansu ya kai dubu 5, sannan sun roƙi Gwamnatin Nijeriya da jihohinsu da a ƙara lura da yanayin da suke ciki, na game da buƙatar samar da abinci, sutura da sauran su. Shi ma Mai’unguwa Malam Nasiru Muhammad, da Nuhu Kaso da Amamatu,  sun nuna jin daɗin sun yi  godiya da addu’ar Allah Ya biya duk mai hannu a ciki.

Ita dai Rayuwar Mata ƙungiya ce ta addini da ta duƙufa wajen ganin sun shareware mata da sauran bayin Allah hawaye musammman almajirai, zawarawa, da sauran mabuƙata. Yayin da ita kuma Gidauniyar Zakka da ke ɗaukar nauyin gudanar da ayyukan jinƙai ga al’ummar Musulmi na ƙasashen talakawa 30 kamar nahiyar Afirka, a wani ɓangare na ƙoƙarin cimma muradun ƙarni na Majalisar ɗinkin Duniya.