Ƙungiyar SCDGG ta ƙi amincewa da sake naɗin Fatima Shinkafi a hukumar ma’adanai

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar nan mai fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya da shugabanci na gari (SCDGG) da ke da hedikwata a Jihar Zamfara ta nuna damuwa kan yadda Shugaban ƙasa ya tsawaita wa’adin aikin Hajiya Fatima Shinkafi a matsayin Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Ma’adinai ta Ƙasa, inda ƙungiyar ta yi Allah wadai da sake ba ta muƙamin.

Ko’odinetan ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Ibrahim A. Sahabi, ne ya yi tsokacin a taron manema labarai a Gusau, Babbab Birnin Jihar Zamfara, a ranar Litinin.

A cewarsa, Fatima Shinkafi ta yi aiki na tsawon shekaru takwas a matsayin Babbar Sakatariyar hukumar, inda wa’adinta zai kare a ranar 24 ga Mayu, 2025.

Ya ce, sakatariyar ta yi wa’adi biyu ba tare da tsinana wani abu ba ga al’ummarta na Zamfara wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idojin jam’iyyar APC da kuma Shugaba Bola Tinubu.

Ƙungiyar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da Ministan Ma’adanai da su dawo da matakin da ya ɗauka na naɗin Hon. Yazid Shehu Ɗanfulani a matsayin Babban Sakataren Ma’adinai da kuma sallamar Fatima Shinkafi daga muƙamin.

Ya ƙara da cewa, Hon. Yazid Ɗanfulani ya taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan jin-ƙai da suka inganta rayukan talakawa a Zamfara.

“Hon. Yazid Ɗanfulani ya taka rawar gani wajen biyawa alummar Gidan gyaran hali basussuka, samar da ayyukan yi, biyan kuɗin asibiti, ci-gaban al’umma kuma, yana da gogewa a harkokin siyasa inda ya haɗa mutane miliyan ɗaya domin yakin neman zaɓen Shugaba Tinubu a 2023 a jihar Zamfara.”

“A matsayinsa na tsohon ma’aikacin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya yi shekaru goma yana yi, Hon. Yazid Ɗanfulani ya nuna ƙwarewa na musamman da kwazo wajen gudanar da ayyukansa wanda ya kai ga ba shi lambobin yabo da dama na cancanta a lokacin aikinsa.”

“A matsayinsa na tsohon kwamishinan kasuwanci da masana’antu a jihar Zamfara, Hon. Yazid ya taka rawar gani wajen bunƙasa tattalin arziƙi, kasuwanci da zuba jari a jihar Zamfara”, inji Kwamared.

“Jagorancinsa da hangen nesansa sun taimaka wajen samar da damammaki ga ƴan kasuwa, da masu ƙananan sana’o’i, wanda hakan ya taimaka wajen haɓaka tattalin arziƙin jiharmu.”

“Saboda haka muke kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya duba lamarin, ya dawo da Hon. Yazid Ɗanfulani a matsayin da ya ba shi tare da sallamar Fatima Shinkafi don ci-gaban Ƙasa da Jihar Zamfara.

Idan za a iya tunawa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana Hon. Yazid Ɗanfulani a matsayin Sakaren Zartarwa a Hukumar kula da sha’anin ma’adinai ta Ƙasa, yayin da sa’o’i kaɗan bayan naɗin nashi, aka sauya shi da ita Fatima Shinkafi wanda kuma hakan ya jawo cecekuce a ƙasar.