Ƙungiyar SCI ta buƙaci a inganta rayuwar yara masu nakasa

Manhaja logo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ‘Save the Children International’ (SCI) a Nijeriya a ranar Laraba ta yi kira ga hukumomi a Nijeriya da su ɗauki ƙwararan matakai na kare yara masu nakasa.

Daraktar SCI ta ƙasa, Mercy Gichuhi ta bayyana haka a cikin wata sanarwa a Abuja cewa, akwai buƙatar a haskaka halin da waɗannan yara ke ciki.

Gichuhi ta ce, “taron duniya kan nakasassu da aka gudanarwa a watan Fabrairu na da nufin jawo hankalin duniya tare da mai da hankali kan wuraren da aka yi watsi da su, da dai sauransu.

Ta kuma ce, yana da niyyar magance ci gaba mai ɗorewa tare da ƙarfafa ƙarfin ƙungiyoyi.

Gichuhi ta buƙaci masu ruwa da tsaki a dukkan matakai da suka haɗa kai da gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi wajen samar da yanayi mai dacewa da haɗa kan yara masu nakasa.

Da ta ke ambaton hukumar UNFPA ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta 2021, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da rahoton Bankin Duniya kan nakasa, ta ce, “Nijeriya na ɗauke da nakasassu kimanin miliyan 32, waɗanda yawancinsu yara ne.”

A cewar Gichuhi, yara da mata masu nakasa su ne suka fi fama da rashin galihu a lokutan bala’i, rikice-rikice na makamai ko kuma matsalolin jin ƙai.

Ta ce, ana yawan samunsu a sassan daban-daban na ƙasar, kuma da yawansu ba a kula da su yadda ya kamata.

Gichuhi ta ce, ci gaban al’umma ba zai cika ba idan ba a haɗa da magance haƙƙi da buƙatun nakasassu ba.

“Saboda haka, ina kira ga hukumomi, masu ba da gudummawa, kamfanoni masu zaman kansu, jihohi da gwamnatoci da su yi la’akari da haƙƙin nakasassu a cikin tsare-tsare, ba da kuɗaɗe da ayyukan jin ƙai da aiwatar da ayyukan ci gaba,” inji ta.

Gichuhi ta kuma yi kira ga gwamnati da ta tsara shirye-shiryen kiwon lafiya da ilimi da kuma samar da zaman lafiya da za su haɗa kai da kuma ba da dama a wani yunƙuri na daƙile wariyar launin fata da nakasassu ke fuskanta musamman ’ya’ya mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *