Ƙungiyar TOKAN a shirye ta ke ta bai wa manufofin gwamnati goyon baya – Rayyan Yusuf

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban ƙungiyar TOKAN, wadda a Turance a ake kira ‘Trycles Operators Association Kano State’ na jihar Kano, Alhaji Rayyan Yusuf ya bayyana haɗe ƙungiyoyin mamallaka da matuƙa baburan Adaidaita sahu domin yin  magana da murya ɗaya abune mai kyau da Gwamnatin jihar Kano ta yi.

Ya yi nuni da cewa a baya ma an taɓa makamancin hakan, kuma su masu baiwa manufofin Gwamnati  goyon baya ne don haka wannan abune mai kyau da suke murna dashi  don zai taimaka wajen  inganta abinda suke domin amfanin al’umma.

Alhaji Rayyan ya yi nuni da cewa samar da wannan ƙungiya da ƙungiyoyin Adaidaita sahu za su riƙa magana da yawun ɗaya ba yana nufin an rusa ƙungiyoyin bane, kowacce ƙungiya tana nan a matsayinta,yanzu dai anyi  musu shugabanci ne kamar a ƙarƙashin lema da  kowace ƙungiya take ciki,sannan idan Gwamnati zata sauko da wani abu ga ƙungiyoyin yan Adaidaita ko wani abu da za a yi zata kirawo shugabancin “ɓOTORA” ta faɗi abinda za a yi.

Ya bada misali da cewa kamar a baya ne, “TOKAN” ƙungiyoyi ne guda Bakwai aka haɗe su aka bada sakataren daga ɓangaren Gwmnati aka yarda sun zama ɗaya, sannan aka yi zaɓe shugabansu na farko shine Sani Sa’idu ɗankoli shi kuma ya yi masa mataimaki ya yi wa’adi biyu ya sauka shi kuma ya zama shugabanta na yanzu.

Alhaji Rayyan Yusuf ya ce don haka wannan tsari da akayi na samar musu da murya ɗaya a ƙarƙashin shugabancin riƙo na  Kwamred Nazifi BK.Gidan Kuɗi suna fata in Allah ya yarda zai zame musu alkhairi gaba ɗaya tun daga kan su shugabannin ƙungiyoyin Adaidaita sahu da masu jan baburan da mamallaka.

Ya yi kira ga sabbin shugabannin na “ɓOTORA” akan yin riƙo da gaskiya da adalci hakan zai sa mambobi su gamsu da irin manufofi da ake so a cimma da zai kyautata harkokinsu.

Shugaban ƙungiyar na TOKAN.Alhaji Rayyan  Yusuf  ya ce su a ƙungiyance a shirye suke su bada gudunmuwa ga Gwamnati ko da na dawo da karɓar haraji mai sauƙi ne,daga mambobinsu domin zai riƙa taimaka mata wajen aikace -aikace da al’umma ke cin gajiyarsu  na gyaran hanyoyi da sanya fitilu, don ance suma su zo su bayar da haraji ba laifi bane.

Alhaji Rayyan Yusuf ya yi kira ga yan ƙungiyoyin su na baburan Adaidaita sahu dama sauran jama’a su zama masu kiyaye doka su kuma a ƙungiyance zasu baiwa Gwamnatin haɗin kai da goyon baya a kowane lokaci  domin a cimma nasarar abinda ake nema.