Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take.

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar Aminu Ahmed Getso ya sanyawa hannu a litinin din nan.

Getso ya bayyana kyara, cin mutunci da tsangwama da ya ce wakilan nasu na fuskanta daga gwamnati da wakilanta yayin gudanar da aiyukansu a fadin jihar.

Kazalika ƙungiyar ta koka kan yadda ta ce, gwamnatin na amfani da waɗanda ba yan yaridu ba wajen ɗaukar harkokin gwamnati, maimakon barin yan jaridu su yi aikinsu bisa ƙwarewa.

A saboda haka ne ƙungiyar ta ce daga yanzu ba zata sake halartar taron yan jaridu, ko wata ganawa da wakilan gwamnati ba, har sai an samu gyara kan ‘yanci da kuma kare lafiyar yan jaridu a faɗin jihar.