Ƙungiyar ’yan fim ta Arewa ta zaɓi Sani Sule Katsina a matsayin sabon shugabanta

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Ƙungiyar masu shirya fim ta Arewa, wato Arewa Film Makers Association Of Nigeria, ta gudanar da sabon zaɓen shugabannin da za su tafiyar da shugabancin ta na gaba a taron da ta gudanar a ranar Lahadin makon jiya.

Taron wanda aka gudanar da shi da yammacin ranar Lahadi, 23/1/2022 a wajen taro na Hazeen Event Center da ke cibiyar digan gona a cikin garin Kano, ya samu halarta dukkan wakilai daga jihohin arewacin ƙasar nan da sauran masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.

Tun da farko da yake bayanin yadda taron ya gudana, shugaban kwamitin shirya zaɓen Mika’ilu ibn Hassan Gidigo, ya ce, “Wannan zaɓen an shirya shi ne don ya kasance ‘yan ƙungiyar ne kaɗai su ke da haƙƙin su yi zaɓe, don haka babu wani da ya shiga cikin masu zaɓen, hakan ta sa mu ka yi zaɓen cikin kwanciyar hankali, mu ka gama lafiya.

Mu na fatan waɗanda aka zaɓa za su gudanar da shugabancin su cikin adalci domin saboda hakan ne ya sa aka duba nagartar su aka zaɓe su.”

A ɓangaren sunayen shugabannin da aka zaɓa kuwa, sun zaɓi Sani Sule Katsina Shugaba, Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, Mataimakiyar Shugaba ta ɗaya, Wash Waziri Hong Mataimakin Shugaba na biyu, Alhaji Habibu Baffa Jalingo Mataimakin Shugaba na uku, Salisu Officer Sakataren ƙungiya na ƙasa, Comr MB Mukhtar Ma’ajin ƙungiyar. 

Sauran waɗanda aka zaɓa ɗin sun haɗa da; Jamilu Ahmad Yakasai, Amina Adamu, Nasiru B A Hassan, Audu Boda, Mahmoud Mukhtar, Daneji Yahaya B Abubakar, Jamila Nagudu, Hadiza Muhammad, Hamza Jibril da Halima Muhammad.

Da mu ke tattaunawa da shi bayan kammala zaɓen, sabon shugaban ƙungiyar ta Arewa Sani Sule Katsina, ke Jawabi bayan zaɓen sa da aka yi a matsayin sabon shugaban ƙungiyar Sani Sule Katsina, Ya bayyana farin cikin sa da kuma godiya ga Allah bisa wannan zaɓin na sa da aka yi a matsayin shugaban ƙungiyar, sannan ya yi alƙawarin gudanar da shugabancin na sa bisa gaskiya da kuma yardar ‘yan ƙungiyar in da ya ci gaba da cewa, “Daman ni ba baƙo ba ne a shugabancin wannan ƙungiyar, domin tsawon lokaci ina a matsayin Sakataren ta na ƙasa.

“Don haka na san wahalar ta na kuma san daɗin ta, domin mu mu ka kafa ta, saboda haka duk wani abu da za a iya gani kuma za a kawo nasara ko kuma wani abu da aka fara za mu yi iya ƙoƙarin mu don mu ga mun samar da shi, domin kuwa sun ga na dace ne shi ya sa suka ba ni shawarar na nemi shugabancin, kuma har Allah ya sa ga shi a yanzu mun kai ga nasara, domin kuwa ganin na fito ne ma ya sa wasu suka janye ba su tsaya takarar ba, kuma ita wannan ƙungiyar ta mu mutane sun san da irin cigaban da ta kawo tsawon lokaci a wannan masana’antar, don haka a yanzu mun samu wani ƙarfin gwiwa na tunanin ya za mu yi mu ci gaba da kawo abubuwan da mu ka saba yi a baya, Wannan ce ta sa ma da jama’a suka kawo shawarar na tsaya shi ya sa na tsaya ɗin don mu ga mun kawo cigaban, kuma in Allah ya yarda mu na da sabbin tsare-tsare da mu ke da su da za su kawo cigaban.”

Dangane da yadda kasuwancin fim yake kuwa a yanzu cewa ya yi, ” wannan mai sauƙi ne, domin kowa ya sani ina ɗaya daga cikin mutanen da suka fara yin gaba wajen samar da kasuwanci na zamani a cikin masana’antar mu, don tun da daɗewa lokacin da ana CD ni na daɗe da tafiya harkokin kasuwancin zamani in da na ƙulla alaƙa da manyan gidajen talbijin kuma na shiga harkar ‘online’, don haka na san harkar, kuma mun san yadda za mu fahimtar da mutane su gane, waɗanda suke ganin harkar ta taɓarɓare za mu ɗora su a kan hanyar da za su samu abin da ya fi wanda suke tsammani. “

A game da alaƙar ‘yan fim da gwamnati kuwa cewa ya yi, ” To mu na da kyakyawar alaƙa da gwamnati,  abubuwan da suke faruwa ana komawa gefe ne a zauna don haka gwamnatin ba ta fahimtar abin da a ke yi, amma in Allah ya yarda a wannan lokacin za mu isar wa da gwamnati irin gudunmawar da mu ke bai wa jama’a, musamman yara matasa, saboda rage masu zaman banza ma a cikin jama’a wani abu ne, don ka taimaki gwamnatin, don haka mu na fatan za mu samu kyakyawar fahimta a tsakanin mu da gwamnati ta sama da ta ƙasa.”

Daga ƙarshe ya nemi haɗin kan ‘yan ƙungiyar wajen ba shi goyon baya domin ya samu ya kai ga cimma burinsa, kuma ya yi fatan alheri ga dukkan jama’ar da suka zaɓe shi da sauran waɗanda suka bada ta su gudunmawa wajen ganin zaɓen ya kammala cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *