Ƙungiyar ’yan sintiri ta ja kunnen masu yi mata sojan-gona

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ‘Yan Sintiri ta ‘Vigilante Group of Nigeria VGN’ ta ƙasa ta ja kunnen masu amfanin da sunan ta, suna nuna kan su a matsayin mambobi, alhali su ba ‘yan ƙungiyar ba ne, inda ta ce za ta ɗauki duk matakin da ya dace a kan wanda aka kama.

Ƙungiyar ta ce, duk wanda ya san shi ba ɗan wannan ƙungiya ba ne, to ya daina amfani da suna, ko kaki, ko duk wani alami na wannan ƙungiya.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa ta ƁGN, Kaftin na sojan ruwa (mai ritaya), Abubakar Umar Bakori ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira Kaduna cikin makon nan, inda ya ce, “Haramun ne mutum ya yi amfani da kayan mu, in shi ba mamban mu ba ne, duk wanda muka kama, za mu kai shi kotu.”

A nan ne shugaban ya yi ƙarin haske da cewa wannan ƙungiya ta su, ba wai ƙungiya ce ta neman kuɗi ba, ƙungiya ce taimakon ƙasa da al’umma. Ya ce, wajibi ne kowane ɗan ƙasa ya duba ya ga ta ina zai iya bayar da gudumawa don ci gaban ƙasa. Shi ne su suke bayarwa ta harkar tsaro.

Da ya ke bayani game da wanda ya je kotu da ƙungiyar, wato Alhaji Usman Jahun kuwa, Kwamanda Bakori cewa ya yi, “Shi mun dakatar da shi, shi kaɗai muka dakatar. Wannan a rubuce ya ke, mu tura ma duk jami’an tsaro, cewa mun dakatar da shi, saboda akwai binciken da Hukumar EFCC ke yi a kan shi, bisa wani koke da muka shigar.”

Ganin cewa akwai yunƙurin da aka jima ana yi don ganin Majalisar tarayya ta yi dokar samar da wannan ƙungiya ta ‘yan Ɓigilantee, wato bill. Ina aka kwana? Sai Kwamanda Bakori ya ce, “Batun bill yana ofishin shugaban ƙasa. Yanzu saboda an samu sabuwar gwamnati, dole sai mun sake mayar wa Majalisa. Kuma alhamdu lillahi, ba a taɓa watsi da bill ɗin mu ba, sai dai maganar gyare-gyare, kuma ana nan ana yi.”

Tun farko a jawabin sa ga manema labaran, Alhaji Bakori cewa ya yi, “Abin da ya sa na kira wannan taron manema labarai a yau shi ne, saboda shekaru 14 da muka yi muna Shari’a game da wannan ƙungiyar ta ‘yan sintiri na ƙasa baki ɗaya. Ba da ni aka fara wannan rigimar ba, na gaje ta ne. Sun shekara 12 suna Shari’a tsakanin Marigayi Alhaji Ali Sakkwato (Allah ya ji kan sa), da wanda ya nemi ya ƙwace ƙungiyar daga hannun sa, Alhaji  Jahun. 

“Sun fara wannan Shari’a tun daga Majistare, aka je babbar kotun taraya, aka je kotun ɗaukaka ƙara, har zuwa kotun ƙoli. A kotun ƙoli ne sai Allah ya yi wa Alhaji Ali Sakkwato rasuwa. Sai ya zama kuma a cikin wannan Shari’a da ake yi, sam babu sunan ƙungiya a ciki, ni ma ba ni a ciki, tsakanin wasu mutane 13 ne da Alhaji Ali. 

“Saboda haka rasuwar sa sai ta kashe magana, saboda ba za a iya ci gaba da Shari’a ba. Don haka sai shugabannin ƙungiyar na ƙasa suka kira babban zama na ƙasa. A zaman ne aka ce a zaɓi sabon shugaba. Ba na wurin wannan zama, amma sai suka yarda cewa Allah ya nufa ni ne zan karɓi ragamar shugabancin.”

Daga nan sai Alhaji Bakori ya ci gaba da bayyana cewa, bayan ya karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar, ya kira duk ɓangarorin biyu, ya ce masu kowa ya kawo abin da ke hannun sa na ƙungiya, ɓangaren Alhaji Ali suka kawo nasu, amma shi ɓangaren Jahun sai suka ƙi. 

“Daga nan ne sai muka kafa Kwamitin bincike don mu gano ko akwai wani abin da ya kamata a magance, saboda mu ci gaba da aiki, nan ma Jahun ya ƙi yarda ya haɗa kai. 

Daga nan sai kawai sabon shugaban ya shiga harkar aiki don ciyar da ƙungiya gaba. Inda ya fara da batun samar da babban ofishin su na ƙasa a Abuja, wanda haka ne da ma ya dace. Suka rubuta wa hukumar yi wa kamfanoni rajista don canja wannan adireshi daga Kaduna zuwa Abuja, inda kuma suka biya hukumar ta CAC bashin da ake bin ƙungiyar har na tsawo shekara 24.

Baya ga canjin ofishin su na ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja, Alhaji Bakori ya samu damar gudanar da wasu canje-canje na ganin ƙungiyar ta zauna da gindin ta, waɗanda suka haɗa da yi wa logon su rajista da dai sauran kayan ƙungiyar. 

Ya ce, yana cikin gudanar da waɗannan gyare-gyare ne sai kawai shi Jahun ya kai shi ƙara, inda bayan da aka fara Shari’a, bisa hujjojin da Alhaji Bakori ya bayar, sai shi da kan shi Jahun ɗin ya janye ƙarar, “Yanzu Ɓigilantee ta zama ɗaya,” inji Bakori.