Ƙungiyar ’yan Tifa ta tallafa wa marayu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar ’yan Tifa ta Jihar Kano ta raba kayayyakin abinci, har da ma tufafi ga ’ya’yan ’yan ƙungiyar da su ka rasu sama da guda 100 a ranar Litinin da ta gabata a ofishinta na jiha.

Hakimin Ƙaramar Hukumar Garinmallam, wanda ya samu wakilcin Wazirin Garin Malam Sheik Abubakar Rabo Abdulkarim, shi ne ya jagoranci rabon kayan.

Sheikh Abdulkarim ya ce, sanya farin ciki a zukatan marayu da taimaka wa rayuwarsu abu ne wanda zai inganta rayuwar su, tare da kawar musu da tunanin rashin iyayen su.

Ya bayyana cewa, halin da marayu da iyayen su suke ciki abu ne na a tausaya musu, musamman yadda su ke kwana babu abinci da kuma yadda ba sa iya zuwa makaranta.

Shi ma a nasa jawabin, Dattijon Kungiyar Alhaji Ali Babba Ɗan Agundi, ya ja hankalin ’ya’yan ƙungiyar Tifa na Jihar Kano da su cigaba da kawo aikin cigaba a ƙungiyar, tare da ɗaukar nauyin marayun da a ka mutu anka barsu, musamman marayun ’ya’yan ƙungiyar.

“Wannan matakin da ku ka ɗauka matakine da zai taimaka muku kuma ya ƙara ƙauna a tsakanin ku, kuma irin wannan aikin na daga cikin ayyukan da Allah ya ke so, wato taimakawa marayu,” inji shi.

Tunda fari, a jawabin da ya gabatar na makasudin tallafain Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ’yan Tifa na Ƙasa kuma shugaba na jiha Kwamared Mamunu Ibrahim Takai, ya ce, sun zaɓi marayu 101 da iyayensu ke sana’ar yashi, ƙasa da dutse domin basu tallafin.

“Mun tallafawa Waɗannan yara ne sakamakon yadda su ka rasa mahaifansu, kuma mun fahimci su na buƙatar taimako tunda muma wata rana za mu koma ga mahaliccimmu kuma za mu so muma a kula da ‘ya’yanmu”, inji Mamunu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *