Daga CMG Hausa
Manya da ƙananan ofisoshin jakadancin ƙasar Sin dake sassan daban-daban na duniya, sun gudanar da bikin murnar cika shekaru 73 da kafuwar Jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, yayin da wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka bayyana fatansu na alheri ga babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 dake tafe da ƙara fatan yin haɗin gwiwa.
Babbar darektar ofishin MƊD dake Geneva Tatiana Valovaya, da babban darektan hukumar kare ‘yancin mallakar fasaha ta duniya Daren Tang, da babban darektan ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa Guy Ryder, da babbar darektar ƙungiyar cinikayya ta duniya Ngozi Okonjo-Iweala, da sauran shugabannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da wakilan din-din-din na ƙasashe daban-daban dake Geneva, duk sun bayyana jin daɗinsu tare da yaba irin ɗimbin nasarorin da ƙasar Sin ta cimma cikin shekaru 10 da suka gabata, inda suka yi fatan za a gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara.
Sun kuma bayyana fatan ci gaba da zurfafa haɗin gwiwa da ƙasar Sin a fannoni daban-daban, tare da fatan ƙasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin ƙasa da ƙasa, da ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya da bunƙasuwar duniya.
Mai fassara: Ibrahim