Ƙungiyoyin ƙwadago sun jinginar da aniyar shiga yajin aiki, yayin da ƙarin albashi na N35,000 zai fara aiki daga Satumba

Ƙungiyar ƙwadago NLC da takwararta TUC, sun jinginar da aniyarsu ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani na tsawon wata guda.

Hakan na ƙunshe ne cikin takardar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ɓangaren gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin a taron da suka yi ranar Litinin.

Yayin zaman nasu, Gwamnatin Tarayya ta yi tayin ƙarin albashi na N35,000 amma ga ma’aikatanta kaɗai wanda zai fara aiki daga watan Satumba zuwa lokacin da za a rataɓɓa hannu kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Tuni dai sugabannin ƙungiyar Maritime Workers Union of Nigeria (MWUN) suka umarci mambobinsu da su koma bakin a tashoshin jirgin ruwan da ke sassan ƙasa.

Da fari ƙungiyar ta bada odar rufe duka tashoshin jirgin ruwa da sauransu a matsayin cika unarnin ƙungiyar ƙwadago don shiga yajin aikin da aka shirya farawa a Talatar wannan makon.