Ƙungiyoyin cinikayya na Sin sun tafi waje don neman jari

DAGA CMG HAUSA

Kwanan baya, kasar Sin ta sauya manufarta ta kandagarkin cutar COVID-19 bisa halin da ake ciki, hakan ya sa kamfanoni masu cinikin shige da fice na wuraren daban-daban na kasar Sin suka yi hayar jiragen sama na musamman domin fita waje neman jari.

Ya zuwa yanzu, larduna 9, cikinsu har da Guangdong da Zhejiang da Jiangsu da Fujian da sauransu, sun kafa kungiyoyi ko hukumomin cinikin shige da fice, da nufin zuwa kasashen waje don habaka kasuwa da neman kwangiloli.

Tun daga watan Yulin bana, birnin Ningbo na lardin Zhejiang ya kafa kungiyoyi a ko wace wata, wuraren da kungiyoyin suka ziyarta sun hada da Italiya da Indonesiya da UAE da Japan da sauran kasashe da wurare, kuma yawan kudaden dake shafar ciniki tsakaninsu ya kai dala biliyan 2.

Ban da wuraren dake dab da teku, wasu larduna dake nesa da teku ciki hadda lardin Sichuang, wanda ya kasance lardi mafi karfin tattalin arziki a yammacin kasar Sin, ya fara tura tawagoginsa zuwa ketare. A ran 5 ga wannan wata, mutane 40 daga kamfanoni 31 dake shafar sana’o’in abinci da magunguna da motoci da kayayyakin gida da na gona, sun tafi Faransa da Jamus da Italiya, don gabatar da biki na kwanaki 9 domin ingiza ciniki tsakanin kamfanoninsu da wadannan kasashe.

Mai fassara: Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *