Ƙungiyoyin Dawakin Tofa sun yi alƙawarin ba gwamnati haɗin kai – Yarima

Daga MUHAMMAD MUJITABA

Ɗaukacin ƙungiyoyi da ɗaukacin al’ummar Dawakin Tofa, ƙarƙashin jagorancin mai girma Sarkin Dawaki mai Tuta na Masarautar Bichi kuma Hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Ismail Ganduje, sun yi alƙawarin ba wa Gwamnatin Tarayya da gwamnatin Jihar Kano haɗin kai kan irin cigaba da ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta ke samu na cigaba kan gine-gine na Makaranto Gwamnatin tarayya da na Jihar Kano a wannan lokaci.

Wannan Jawabin ya fito ne daga bakin Alhaji Abdulahi Ismail Ganduje wanda aka fi sani da Yarima ya bayana a wata hira da manema labarai a Kano a ranar alhamis ta gabata.

Yarima ya ce, yanzu haka ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta samu tagomashi mai yawa daga gwamnatin tarayya na kafa makaranta ta horar da sojojin ruwa da za a gina da kuma makarantar kimiyya da fasaha, ta gwamnatin tarayya wato Federal Poltechnic Dawakin Tofa, ga kuma makarantar kimiyya kenan a Dawakin Tofa, Sai kuam makarantar koyon aikin lafiya ta Gwamnatin Jihar Kano za ta gina a wannan ƙaramar hukuma wanda wannan duk aikin cigaba ne da aka samu a wannan yanki a wannan lokaci.

Haka kuma Yarima ya yaba wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan wannan cigaba da aka samu a wannan lokaci da kuma yaba wa dagatai 38 na wannan ƙaramar hukuma da sauran al’ummar wannan yanki, musamman a lokacin na samara da rijiyar burtsatse da rundunar sojan ruwan Nijeriya ta gina a garin Ganduje da Gwaman Kano ya jagoranci ƙaddamarwa a wannan lokacin da ya gabata.

A ƙarshe dai Yarima ya ce, kan wane ya sa al’umar yankin da wasunsu na yin Addu’ar alkhairi ga gwamnatin tarayya da jiha da kuma fatan zaman lafiya a ƙasarmu Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *