Ƙungiyoyin mata sun shirya tattakin nuna goyan baya ga Gwamnan Kogi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Ƙungiyoyin mata aƙalla 600 da suka fito daga sassa daban-daban na ƙasar nan, sun kammala shirye-shiryen gudanar da tattakin haɗin gwiwa don nuna goyan bayan su ga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Tafiyar haɗin kai da za a yi a ranar Talata mai zuwa a Abuja, babban birnin ƙasar mai taken, “Mata Miliyan Ɗaya don GYB”.

Masu gudanar da aiki ƙarƙashin ƙungiyar Women United For Yahaya Bello (WUYABEL), ƙungiyoyin mata da suka haɗa da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin addini, ƙwararru, mata a kafafen yaɗa labarai, siyasa, matan kasuwa da kuma manyan mata ‘yan kasuwa da dai sauransu, za su mamaye Abuja domin bayyana wa gwamnan goyon baya, musamman a daidai lokacin da al’ummar ƙasar ke shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

A cewar masu shirya taron, ƙungiyoyin mata, bayan sun cimma matsaya a cewa al’ummar ƙasar na buƙatar mutum mai kishin ƙasa, samartaka da iya aiki don maye gurbin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sun ɗauki nauyin haɗa kan su wajen mara wa Gwamna Bello baya, wanda suka ce ya nuna zai iya magance ɗimbin ƙalubalen da ke fuskantar Nijeriya.

Shugabar ƙungiyar ta WUYABEL ta Duniya, Dakta Hannatu Adeeko, ta ce, “taron zai kasance irinsa na farko, musamman yanzu da aka kusa shiga fagen siyasa”.