Ƙungiyoyin mata sun yi kiran a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai

Manhaja logo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu ƙungiyoyin addini masu zaman kansu na mata sun yi kira da a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai da ƙananan yara a ƙasar.

Shugabannin Ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya; Sakatariyar Katolika ta Nijeriya; Ƙungiyar Matan Kirista ta Nijeriya; da kuma Cocin ‘Redeemed Christian Church of God’ sun yi wannan kiran ne a lokacin ziyarar da su ka kai na bada shawarwari ta hanyar Cibiyar Sadarwa da Tasirin zamantakewa, ga mata a wasu yankuna, tare da kira da a inganci abincin da mata ke ci domin su samu damar bai wa jarirai abinci mai gina jiki.

Shugabannin ƙungiyoyin addinin sun yi alƙawarin ba su goyon baya tare da buƙatar aikin haɗin gwiwa don tabbatar da cewa an wayar da kan al’ummomin addini wajen abubuwan da suka shafi mata da ƙananan yara.

Ameerah ta qasa ta ƙungiyar FOMWAN, Rafiah Sanni, ta bayyana farin cikinta game da aikin, inda ta bayyana cewa, ya yi daidai da koyarwar addinin Musulunci ga iyaye mata.

Sanni ta ce, “na yi matuƙar farin ciki da wannan aiki, kuma na yi muku alƙawari da yardar Allah ta musamman za mu haxa kai da kai gaba ɗaya, domin duk abin ake yi a nan yana cikin koyarwar Musulunci ga iyaye mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *