Ƙurajen zafi (1)

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. A yau za mu yi ɗan bayani ne kan ƙurajen da muka fi sani da na zafi, domin sun fi zuwa ne a lokacin da ake tsananin zafi, duk da cewa a wurin wasu waɗannan ƙurajen sun zama al’ada ta fatar jikinsu. Domin ba su da takamaiman lokacin zuwa mu su, ma’ana ko a lokacin da ba na zafi ba za ka iya ganinsu a jikinsu. Da yardar mai dukka, za mu tattauna kan ƙurajen da ma wasu daga cikin hanyoyin da za a iya magance su.

Su dai waɗannan ƙurajen, ƙuraje ne masu zafi da ƙaiƙayi da kuma sanya jiki a yanayi na rashin jin daɗin fatar. Baya ga haka, ƙuraje ne da aka fi haɗuwa da su a lokutan zafi. Wasu na haɗuwa da su ne ta dalilin yawan kwanciya a zafi, ko barci da kaya masu nauyi. Yayin da jikin wasu na samun su ne kawai don lokacin na zafi ne, ko da kuwa sun yi taka-tsantsan tare da bin hanyoyin da za su nisantasu da su.

Su dai waɗannan ƙuraje, an fi ganin su ne a wuya, saman goshi, bayan jiki da kuma hamata. Sai dai a wasu da ba su da yawa su kan same su a ciki da kuma ƙirji.

Akwai jikin da yake saurin yaƙar ƙurajen, saboda dama rashin bin ƙa’idar lokacin ne ya kawo su, don haka a duk lokacin da ya nisanci ababen da muka bayyana a baya, kamar kwanciya cikin zafi ko amfani da kaya masu nauyi sai a nemi ƙurajen a rasa. Sai dai duk da cewa na su masu sauƙi ne, akwai yiwar su tsananta idan an qi bin hanyar rabuwa da su cikin lokaci.

A vangare ɗaya, waɗanda yanayin zafin ne ke kawo masu ƙurajen bin dokokin ba su cika tasiri a wanzuwar ƙurajen ba, saboda dama ba rashin bin ƙa’ida ba ne yake kawo masu su. A na su ɓangaren suna buƙatar hanya da za ta kashe ƙurajen ne, domin jimawan su zai iya kai fata ga wata cutar. Ta yaya? Sanannen abu ne ƙurajen suna da ƙaiƙayi, don haka mai ɗauke da su zai dinga sosawa, wani lokacin har ta kai ga wurin ya ɓare, a bayyanar shimfiɗa ta biyu ta fatar wata ƙwayar cuta za ta samu wurin shiga, daga nan sai labarin ya canza.

Duk da cewa da yawa su kan je asibiti a ba su magunguna na shafawa ko fauda da makamantansu, sai dai a gida ma za ki iya magance matsalar ta bin wasu ‘yan hanyoyi. Amfani da mayuka masu laushi, waɗanda aka yi don kariya daga zafin rana. Amfani da ire-iren su kan kashe ƙurajen. Sai kuma yawan yin wanka. Dama jikin na ƙurajen ne saboda zafi, idan kuwa fata na samun wanka da yawa a irin lokacin sai ta fara canza yanayinta wato daga na zafi zuwa na sanyi, hakan zai iya fatattakar ƙurajen.