Ƙwaƙwalwar ɗan’adam

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan’adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki.

Rubtun yau zai mayar da hankali ne akan ƙwaƙwalwar ɗan adam, baiwar da Allah yayi mata, da wasu daga cikin baye- bayenta. Ƙwƙwalwar ɗan adam tana waɗansu baye-baye da Allah yayi mata a jiki saboda muhimmancinta. Bari na kawo kaɗan daga ciki.

  1. Matsayi: Ƙwaƙwalwar ɗan adam ta kasance a mafi ɗaukakar bigire a jikin ɗan adam. Da Sarkin halitta Ya tashi, sai bai sanya ƙwaƙwalwa a kogon ƙirji ba, ko kogon ƙugu; a a, sai Ya sanya ta a cikin ƙoƙon kai, kuma a bigiren da ta zamo sama da kowace gaɓa a jiki. Sama take da ido, sama take da hanci, baki, da dukkan fuska. Ƙwaƙwalwa sama  take da duk wata gaɓa a jiki. Wannan tsari ya bada ma’ana sosai, saboda bigiren da ƙwaƙwalwa take, da aikin da ta ke yi ya dace da kasancewar ta shugaba ko jagorar gudanarwar gaɓɓan ɗan adam.
  2. Kariya: Sarkin halitta ya bawa ƙwaƙwalwa kariya ta musamman, kamar yadda ya bawa sauran manyan gaɓɓai masu matuƙar muhimmanci irin rasu kariyar. Misali: (a) Zuciya tana cikin kariyar ƙasusuwan haƙarƙari. (b) Jariri ko jaririya lokacin da suke cikin uwa, akwai kariya ta musamman da Allah yayi musu. Shi yasa a cikin littafi mai girma Ubangijin halitta yake cewa: “Mun halicci ɗan’adam cikin duffai 3”. A kimiyyace, jinjiri a kewaye yake da abubuwa guda 3: Na ɗaya, bangon cikin uwa; na biyu, bangon mahaifa; na uku itace jakar paya wadda ta kewaye jaririn. Kuma kowacce gaɓa da muka lissafa anan, hijabi ce kuma kariya ga jinjirin da ke ciki. 
    To haka ita ma ƙwaƙwalwa Allah ya bata kariya sosai. Kamar yadda na ce, a cikin ƙoƙon kai take, Wanda a turance ake kira da “skull”. Yadda wannan ƙashi yake da ƙwari ma wasu masanan na cewa ya kai ƙwarin kankare na gini!

Bayan kariyar ƙashi, ƙwaƙwalwa na kariyar tantani har ruɓi uku(3). Sannan bayan wannan, hanyoyin jinin da suka baibaye ta na da shamaki tsakaninsu da ƙwaƙwalwa, don gudun kada wani abu ya biyo jini, daga nan kuma ya faɗa ƙwaƙwalwa. Saboda tasirin wannan kariya, har ma wasu magugunan cutukan ƙwaƙwalwa kan gaza isa cikin ta, matuƙar dai mutum ta baki ya sha ƙwayar maganin ko kuma allurar maganin akayi masa/mata.
 

  1. Tasaruffi: Ubangijin halittu ya bawa ƙwaƙwalwa dama da iya sarrafa sauran gaɓɓan ɗan’adam. Duk da cewa wannan bayani ya kamata in kawo shi a sashen ayyuka da ƙwaƙwalwa ke yi, to amma ya fi dacewa in sanya shi a nan. A kafatanin jiki, babu wata gaɓa da ke sarrafa dukkan gaɓɓai idan ba ita ba. Hamma, atishawa, miƙa,  yunwa, duk da  hannunta a ciki. Babu yadda za ayi ace wai ƙodarka ta kula da yanayin numfashinka, ko ta shirya tsare tsare na narka abincin da ka ci! Wannan aiki sai ƙwaƙwalwa.
  2. Tsari: wato
    ƙwaƙwalwar ɗan Adam tana da tsari mai matuƙar ban sha’awa. Tana tsara abu daki daki, daga wannan sai wannan. Shi ya sa mutum ya fi sauran halittu hankali saboda ƙwaƙwalwarsa na iya tsara masa abubuwa daki-daki. Misali, abu mafi muhimmanci da ta fi bashi kulawa shi ne sukuni! Duk abinda za ka aiwatar, matuƙar ba sukuni a ciki, to a mafi yawan lokaci, kwaƙwalwar ka zata ta iya haƙura da wannan abu ko meye shi. Misali, kana jin bacci sosai, ga kuma kana so kayi karatun makaranta,  ba ka yi aune ba, za ka iya jin bacci ya kwashe ka. Ko kuma kina tare da ƙawarki kuna hira mai dadi, amma kuma rabon ki da abinci tun jiya da yamma. Akwai gaɓar da za a je dole ke katse hirar, ki nemi abinci domin ki kori tabahuwa!
  3. Ɗabi’a: Allah ya halicci ƙwaƙwalwar ɗan’adam domin ta gane abubuwa saboda ta sauƙaka wa ɗan’adam gudanar da sauran harkoki na rayuwarsa. Da zarar kayi wani abu sau ɗaya, biyu, uku, huɗu, to fa ƙwaƙwalwar ka za ta ɗauki haske cewa wannan abu ana buƙatar sa a rayuwa, saboda haka sai ta fara mayar da shi ɗabi ‘a; sawa’un abun nan nai kyau ne ko akasi haka. Duk inda ɗan Adam ya samu wata biyu zuwa uku, ya na yin wani abu kullum, ta abun zai zama dabi’a. Mutum zai dinga gudanar da wannan abu ba tare da ya yi dogon tunani ba.  Misali idan ɗan adam ya koyi tafiya, sa zarar ya iya to ya dena tunani akan ya ake ayi tafiya. Ƙwaƙwalwar sa tuni ta ɗau hakske, ta adana dukkan bayanan yadda ake tafiya. To da zarar ya tashi zai yi tafiya, sai kawai ƙwaƙwalwar ta bijiro da wannan bayani ta kuma yi tasarrufinsa, ba tare da wani tunani ba.
     
  4. Azanci: Ɗan Adam yana da fifiko akan sauran dabbobi saboda azancinsa. Wato kamar “creativity” kenan a turance. Azancin ɗan Adam na cikin ƙwaƙwalwarsa. Kuma wannan baiwa ta azanci ta taimakawa ɗan Adam wajen zama abinda ya zama a yau. A tarihin ɗan Adam, ya kasance yana bijiro da dabaru kala-kala waɗanda za su taimake shi wajen saukaƙa rayuwarsa, da kuma tabbatar da sukuni. Ɗan Adam ya ƙirƙiri abubuwa da dama ta hanyar amfani da azancin ƙwaƙwalwar sa kamar su: Gina gida, ƙera mota, ɗinka kaya, haɗa kujera, gado, kwalla,  matashi. A wannan zamani,  azancin ƙwaƙwalwar ɗan Adam wanda Allah ya bashi, ya sa ya iya ƙirƙirar jirgin sama,  kwamfuta, wayar salula, Injin wankin kaya, injin cire kudi, na’urar tiyata, da makamantansu.
     
  5. Hikima: sabin kowa ne cewa, duk wani mai hikima, to tabbas yana da kaifin ƙwaƙwalwa. Kuma Ubangiji na cewa:” duk Wanda a ka bashi hikima to haƙiƙa an bashi alkhairi mai girma.” Wannan na ɗaya daga cikin baiwar sa Allah yayi wa ƙwaƙwalwa akan sauran gaɓɓai. To ta ina ake samun hikima? Ta hanyar ilimi, da kuma goayya da na gaba, waɗanda suka san rayuwa. Iya ilininka, iya hikimarka! Shi ya sa ba son ɗan Adam ya dena neman ilimi. Saboda ilimi yana da tasiri ga hankali, da hikima, da azancin ƙwaƙwalwa.
  6. Adani: ita ƙwaƙwalwar ɗan Adam, duk yadda za ta yi, za ta yi domin ɗan Adam ya ci gaba da rayuwa . Shi ya sa take taskance bayanai na yadda ake yin abubuwa saboda da zarar ɗan Adam ya buƙaci yin wani abu, to sai dai kawai ta bude wannan taska ko “memory”  ta ɗauko abinda ake buƙata.  Idan mutum ya koyi tuƙin mota, to ba ruwansa da ya sake koya; idan mutum ya koyi magana ko tafiya, to ba ruwansa da ya sake koya,  matuƙar bai samu wata matsala ta haɗari ko gogewar taskar bayanai a ƙwaƙwalwar tasa ba. Adana bayanai masu alaƙa da abubuwan da muke yi kullum a rayuwarmu, shi ke sa ƙwanwalwa ta samar da ɗabi’a.  Amfanin ɗabi’a shine gudanar da ayyukanka ko ayyukanki na yau da kullum cikin sauƙi ba tare da kin tsaya tantama ko shakka ba; irin ki ce :” Ya ma ake shara?”, ko “ya ma ake wanke-wanke.”

Ni yanzu idan zanyi rubutu, wasu lokutan nakan kawar da kaina kuma ina rubutun cikin salula ta, ba tare da na kalli madannan wayar ba. Me yasa? Saboda hakan ya zama jiki, an taskance bayanan yadda zanyi na rubuta “ruwa” ko “Mustapha” a cikin ƙwaƙwalwa ta. Da fatan an gane.

Masu karatu mu haɗu mako mai zuwa idan Allah ya kai mu, domin ci gaba da kawo muku bayani game da jikin ɗan’adam. Kafin nan nake cewa, Assalamu alaikum.