Ƙwaƙwalwar yaro ta fi buƙatar kulawa daga wata shida na haihuwa zuwa shiga firamare – Hauwa Mustapha Babura

“A ƙasashen da suka cigaba suna fara ba yara tarbiyya tun suna ciki”

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

Tabiyyar yara na ɗaya daga cikin manyan buƙatun da kowacce ƙasa mai son cigaba ta ke da buƙata, domin da yara ne ake samun manya, kamar yadda bahaushe ya ce, “yara manyan gobe”, kuma daga manyan ne ake samun ingantacciyar ƙasa ko akasin haka.

Duk da muhimmancin yara a rayuwar al’umma bai sa wasu mutane ɗaukar reno tare da tarbiyyantar da zu a matsayin wani babban aiki ko abinda ke buƙatar sa ido ba, idan ka ɗauki bahaushe a misali, za ka tarar da cewa, yana ganin abin da matuƙar sauƙi wanda hakan kan taimaka wurin miƙa ragamar tarbiyyar a hannun uwa ita ka ɗai.

A ɓangare ɗaya, masana ba su ɗaukar lokacinsu wurin bincike kan buƙatun yara ƙanani, watakila hakan na da alaƙa da yadda gwamnati bata ba su gatan da ya kamata a ce ta ba su ba. A taƙaice rayuwar babba ta fi ta ƙaramin yaron da ke buƙatar agaji fiye da babba muhimmanci a ƙasashe irin namu. Savanin ƙasashen da suka zama allon kallon mu ta fuskar cigaba.

Da wannan ne zan ce za mu yi mamaki idan na sanar da ku cewa, akwai waɗanda ke zuwa karatu, tun daga matakin difloma har digirin digirgir su yi su kan sha’anin da ya jivinci renon ƙananin yara kawai.

Baƙuwarmu ta wannan satin ce zata tabbbtar da wannan zance, domin ta kasance jajirtacciyar mace da ta sadaukar da lokacinta wurin neman ilimin kula da yara ƙanana, don ganin ta bayar da tata gudunmuwa a fuskar samar da manyan gobe da za a yi alfahari da su.

Hajiya Hauwa Mustapha Babura, ƙwararriya ce a ɓangaren renon yara ƙanani inda a halin yanzu ta ke kan digirin ta na uku a ɓangaren ilimin ƙananin yara. A tattaunawar su da Manhaja, Hajiya Hauwa ta bayyana mana yadda bambancin kulawar da yara ƙanane ke samu tsakanin ƙasashe irin namu da kuma ƙasashen da suka samu cigaba kamar Ƙasar Amurka, wadda a halin yanzu ta ke zaune a can. Ta kuma yi mana bayani kan muhimmancin ba wa yara ƙanani kulawa tun a tashin farko. Ku gyara zama, ku sha karatu, don kwankwaɗar ilimin da ke cikin wannan tattaunawa:

MANHAJA: mu fara da jin tarihin baƙuwar tamu.

HAJIYA HAUWA: Sunana Hauwa mustapha Babura wanda aka haifeni a nan Ƙaramar Hukumar Babura da ke Jihar Jigawa. Na yi karatun firamare da sakandare duk ana Jihar Jigawa.

Daga nan bayan kammala sakandare sai Allah ya yi ban ci gaba da karatu a nan Nijeriya ba, ma’ana aka yi min aure bayan kammala sakandare. Bayan auren ne zama ya kawo mu Ƙasar Amurka, a Jihar Mizori.

Bayan zuwan mu sai ya zama na sake shiga makaranta kamar sakandare ta ke inda na samu shaidar GED kamar ‘certificate’ ɗin WAEC ta ke a Nijeriya.

Daga nan na ɗauki shekaru ban ci gaba da karatu ba, saboda shidimar yara. Sai bayan girman su ne na koma karatu, inda na y diploma akan ‘Early Childhood Education:.

Bayan kammalawa, na sake wata diploma, har wa yau dai kan sha’ani na yara, mai suna ‘Child Development’, wato renon yara. To daga nan ne bayan na kammala na shiga jami’a, na karanci ɓangaren kula da yara ɗin dai, a matakin digiri.

Bayan kammala digiri na samu damar ci gaba da karatun digiri na biyu a fannin ‘Teacher Leadership’. Yanzu kaka Ina kan yin digiri na uku akan sha’anin dai na yara, wato ‘Early Childhood Education’.

Menene ake nufi da ilimin yara ƙanana?

To, alhamdul illah. Idan muka ce ilimin yara ƙanana kusan hakan zai kai mu zuwa ga karin maganar nan ta malam Bahaushe ta “yara manya gobe,” amma manyan yau su ne waɗanda kan tallafi yara har su zama ababen alfahari zuwa gaba.

kusan za ka ga duk ƙasashen duniya musamman waɗanda suka yi nisa a cigaba, za ka ga suna ba wa ɓangaren muhimmanci sosai. Wannan zai sa ka ga hatta da mace mai juna biyu, a na tattali da tarairiyar cikinta, don fara shimfiɗa kan tarbiyyantar da abinda zata haifa.

Za su hidimtawa cikin don ganin an haifi yaron cikin ƙoshin lafiya. Daga nan kacokam kulawar yaron zai koma ga iyayenshi, wanda muka sani, su ne makarantar farko ga ‘ya’yansu.

To, idan ka ɗauka a ɓangaren karatu irin namu, za ka ga cewa yana bayar da gudunmuwa matuƙa a tarbiyya ko in ce renon yara, domin a lokacin da yaron da aka haifa ya cika sati shida a duniya, akan kawo mana shi don kula da shi.

Albarkacin wannan karatu, idan ya kasance yaro na tare da wata matsala, tun a yarintar za mu iya gane yana tare da matsala, kuma mu iya gane nau’in matsalar tasa tare kuma da sanin matakin da ya kamata a bi don shawo kan matsalar. Akwai hanyoyin da muke bi wajan ‘training’ ɗin ƙananan yara, don zama abinda ake fata.

Muna ba wa yara kulawa ta musamman, sannan mu kan tabbatar ba mu fifita wani yaro kan wani ba, ta ɓangaren ɗaukaka mai ilimi sosai daga cikin su, ko kiran wani daƙiƙi. A ƙasashen da suka cigaba ko da wasa malami ba zai jefi ɗalibin sa da kalmar daƙiƙi ba.

Dalilin kenan da ya sa ba ma ‘ranking’ yara ƙanana, ta ɓangaren karatu, ma’ana ba a faɗa ko rubuta wanda ya yi na ɗaya, na biyu har zuwa ƙarshe, wannan na ɗaya daga cikin hanyoyin taimaka wa ƙananin yaran.

A ɓangare ɗaya muna ba wa yara dama wajen zavar abinda suke so su zama tun suna ƙanane, don lurar da su muhimmancin su da kuma na zaɓinsu, domin akwai wani bincike na masana da yake nuna cewa, ƙwaƙwalwar yaro ta fi buƙatar kulawa daga wata shida na haihuwar sa zuwa shekarun shiga firamare.

Muna amfani da kayan wasa don ba su damar yin zaɓi. Wasu su ɗauki ƙwallon ƙafa, wasu likitanci, wasu ƙere-ƙere. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ke sa ka ga yaran ƙasashen turawa sun taso da kaifin basira cikin ƙanƙanin lokaci, sakamakon ba su damar yin abinda suke so, dama duk abinda kaga yaro yana yi na karan kansa, to shi ne babban abinda zuciyarsa ta kwaɗaita da shi tun tasowa.

Wannan ne za ka ga idan ka ɗauki yaran turawa idan ka kwatantasu da ire-iren kasashenmu masu tasowa, za ka ga kamar ba su da tarbiyya, saboda wasu dalilai nasu da ke sa a ba yaran dama su yi rayuwa yadda suke so.

Amfanin irin wannan karatu da kuma aikin na kula da ƙananin yara na da yawa, domin hatta likitoci kan yi amfani da masu koyar da yara ƙanana don sanin haƙiƙanin abinda ke damum yaro.

Wane irin tasiri ilimin yara ke da shi a rayuwar yara masu tasowa?

Gaskiyar zance tasirin ‘Early Childhood Education’ ga yara ƙanane abu ne mai girma. Yana da tasiri ba kaɗan ba, musamman idan ka yi duba ko a addinin Musulunci, an yi maganar cewa, idan ka reni yaro da cin zarafin sa, to shi ma zai taso yana irin wannan cin mutuncin ga nagaba da shi.

Idan ka yi duba da ƙasashe na turawa, kamar nan Amurka, suna narka maƙuddan kuɗaɗe wurin samarwa yara ƙanana walwala da kuma nisanta su daga cin zarafi kowane iri ne. Domin ko mu nan a matsayin mu na masu koyar da yara, akwai ‘budget’ na musamman da gwamnati ta ware don walwala da jim daɗin mu.

Ko a sati biyu da suka wuce, gwamnatin Ƙasar Amurka ta ba wa dukkan masu koyar da yara kyautar kuxi daga Dala 3000 zuwa ƙasa. Duk saboda me? Saboda samar da yaran da za su zama sun ci gaba da ciyar da ƙasar gaba.

A wani ɓangare na lafiya ma, za ka tarar da cewa, gwamnati na kula sosai da duk abinda yara za su ci, saboda shi ma yana da nasa tasiri wurin samun yara masu kaifin ƙwaƙwalwa da basira.

Wani abu guda kuma shi ne, hatta iyaye ba su da iko kan ‘ya’yansu kamar yadda gwamnati ke da shi, saboda fahimtar muhimmancin yaran da suka yi, saboda yaro ɗaya idan ya samu kansa a cin zarafi ko razshin tarbiyya, idan ya lalace, to fa al’ummar ƙasar ce za ta samu matsala. Dalilin kenan da ya sa ko a aikin koyar da yara idan za a ɗauke ka, sai ka yi rantsuwa cewa, za ka kula da yaran wurin tunaninsu da ma inganta rayuwarsu.

Kuma ko da wasa idonka ya ga wani cin zarafi ga ƙananin yara, koda kuwa iyayensa ne ke masa, to akwai lambobin waya da gwamnati ta tanada, da za ka kira, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci za su iso, su kawo ɗauki. Za su tabbatar da ɗaukar mataki da zai hana faruwan hakan ga yaron har abada, ciki kuwa har da karɓe shi daga hannun iyayen idan ita ce mafita.

A ɓangare ɗaya, al’ummar ƙasarmu Nijeriya suna da sha’awar kwaikwayo tare da ɗaukar al’adun turawa. Shin kina ganin idan hakan ya ƙara yawaita zai taimaka wurin rage matsalolin da ake fama da su a ƙasar nan?

A nan za mu dakata, kuma da wannan tambayar muke fatan fara samun amsarta daga baƙuwar tamu kafin wasu tambayoyin su biyo baya.

Mu haɗu a sati mai zuwa, don karanta ƙarshen wannnan tattaunawa da Hajiya Hauwa Mustapha Babura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *