Ƙwararru: Shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” na bunƙasa ci gaban nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA

Wasu masu bincike, kuma ƙwararru game da al’amuran ƙasa da kasa na yankin gabashin Afirka, sun bayyana shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” da ƙasar Sin ta gabatar, a matsayin manufar dake ingiza ci gaban nahiyar Afirka.

Ƙwararrun sun yi tsokacin ne a jiya Laraba, yayin taron yini guda da ya gudana ta kafar bidiyo, mai taken “Muhimmancin shawarar ziri ɗaya da hanya daya ga nahiyar Afirka.”

Ɗaya daga cikin ƙwararrun Frederick Golooba Mutebi daga ƙasar Uganda, ya ce shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya, ta zamo ginshikin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da rage matsalar ƙarancin guraben ayyukan yi, da bunƙasa cinikayya da dai sauran su.

Mr. Mutebi ya ce “Sin ba ta da nufin wawashe arzikin Afirka, sabanin yadda ƙasashen yamma ke zargi.

Kuma idan aka dubi ci gaban da nahiyar Afirka ke samu a fannin samar da ababen more rayuwa, za a fahimci irin taimako da shawarar ziri ɗaya da hanya daya ke bai wa nahiyar.

Sin na samar da agaji irin wanda ƙasashen Afirka ke bukata”.

A nasa ɓangare kuwa, masani a fannin alaƙar ƙasa da ƙasa daga ƙasar Kenya Adhere Cavince, cewa ya yi shawarar ziri daya da hanya ɗaya, ta bai wa ƙasar Sin damar raba dabarun ci gaban ta da sauran ƙasashen Afirka masu tasowa.

Ya ce gwamnatin Kenya na aiki ƙut da ƙut da ƙasar Sin, wanda hakan ya haifar da nasarar kammala layin dogo da ya haɗe biranen Mombasa da Nairobi, aikin da ke taka muhimmiyar rawa a fannin bunƙasa ci gaban tattalin arzikin kasar Kenya.

Cavince ya ƙara da cewa, cikin shekaru goma da suka gabata, Sin da ƙasashen Afirka sun zamewa juna abokan hulɗar cinikayya yayin da kuma shawarar ziri daya da hanya ɗaya ta buɗe wa sassan 2 sabbin ƙofofin bunƙasa haɗin gwiwa.

Fassarawar Saminu Alhassan