Ƙwarewa a sana’a ita ce gaba da samun digiri – Dogondaji

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da kafafen yaɗa labarai suke ci gaba da tafka muhawara game da fififkon ilimin digiri a kan sana’a, mun samu zantawa da Malam Yahya Dogondaji wanda matashi ne wanda ya yi wa ‘yanuwansa matasa zarra wajen yaƙi da talauci, ta hanyar yi wa kansa fafutuka da kuma horas da matasa masu dama a ƙarƙashin sana’ar sa ta gyaran waya da kuma samar da guraben ayyuka ga matasa da dama. Hakazalika, ya kasance mai tallafa wa marasa galihu ta gidauniyarsa. Wakiliyar MANHAJA BLUEPRINT, Amina Yusuf Ali ta samu tattaunawa da Malam Yahya Dogon daji, kuma ga yadda tattaunawar ta kasance. A sha karatu lafiya.

MANHAJA BLUEPRINT: Za mu so ka faɗa mana cikakken sunanka.

YAHAYA DOGON DAJI: Bismillahir rahmanir raheem. Sunana Yahaya Dogondaji Abubakar, amma an fi sani na da (Yahaya Dogondaji ) a dalilin na tashi ne a wurin kakannina. Da akwai Alhaji Nuhu Dogondaji da Alhaji Garba Dogondaji. To da wannan dalilin ya sa ake kirana da Yahya Dogon daji. Anan ne na samo wannan sunan, Yahaya Dogondaji.
Waye Yahya Dogon daji?

To, alhamdulillahi. Kamar yadda na faxa a baya, sunana Yahaya Dogondaji, kuma an haife ni a qauyen Marafa, a gundumar Mahuta, a yankin Masarautar Zuru. Nayi Karatun firamare a Sakkwato, har zuwa Sakandari. Bayan na kammala Sakandare a 2009, na samu nasarar zuwa kwalejin fasaha ta Sokoto (Sokoto State Polytechnic), inda na yi karatun difloma a fannin kimiyyar kwamfuta (National Diploma in Computer science).

Lokacin da na kammala Polytechnic ɗin, sai na zarce jami’ar Usman ɗan Fodiyo (Usmanu Ɗanfodiyo University) duk dai a nan birnin Sakkwato. inda a nan ne na samu nasarar samun digiri na farko a (Hausa), a shekarar 2017. Alhamdulillahi, yanzu na yi aure, kuma Alhamdulillahi har na samu ɗiya.

Malam Yahya wacce sana’a kake yi a halin yanzu?

A halin yanzu dai ina sana’ar gyaran wayar salula a nan kasuwar hada-hadar wayar salula dake unguwar Hajiya Halima Area Sokoto, a nan birnin Sakkwato.

Tun yaushe ka fara wannan sana’a ta gyaran waya?

Na fara wannan sana’ar tun a shekara 2019 a lokacin da na kammala sakandare.

Duba da sana’o’i da muke da su birjik a Birnin Shehu da ma arewacin Nijeriya bakiɗaya, me ya ja hankalinka, ko na ce me ya sa ka zavi sana’ar nan ta gyaran waya?

Eehhh, tabbas haka ne. A jahar Sakkwato akwai sana’o’i iri-iri na zamani sai ga shi na zavi ita wannnan sana’ar. Gaskiya ba wani dalili ba ne, illa tunda na taso a rayuwata, na tsinci kaina acikin sha’awar kwamfutoci da sauran kayan zamani wato kayan lantarki. Tun ina ɗan yaro nake tava cinikin kayan electronics kamar su TV, rediyo da sauran su. Wannnan ne ya taimaka har na tsinci kaina a wannan sana’ar.
Kuma abinda mutane ba su gano ba, sana’ar gyaran waya sana’a ce mai sirri sosai. Akwai alkhairi mai yawa a cikinta. Ba ƙaramin rufin asiri ake samu ba.

Bayan wannan sana’a ta gyaran waya, shin akwai kuma wasu abubuwan da kake yi don ƙarin samun kuɗaɗen shiga a ɓangarenka ko don taimaka wa al’umma?

Tabbas akwai. Ina noma domin na gaji sana’ar noma daga wurin iyaye da kakannina. Bayan wannan kuma, ina yin aikin saƙa, (Humanitarian assistance) wato ba da aikin jinkai da taimaka wa alumma, musammar gajiyayyu, mabuƙata da su kansu matasa. Duk inda na ga wata matsala ko damuwa to tabbas naka tsaya na tabbatar da na bada tawa gudummuwa domin ceto ko taimka wa rayuwar mabuƙata.

A halin yanzu kana da wasu mutane ko yara waɗanda suke aiki a ƙarƙashinka, ko waɗanda suke koyon sana’ar daga gare ka?

Tabbas inada su. Ina tabbata muku cewa ni Yahaya Dogondaji na horar da matasa fiye da 1000 a ita wannnan sana’ar gyaran wayar salula. Na horar da matasa a nan gida Nijeriya da ma ƙasar Nijar. Labaran suna nan a internet da wasu gidajen jaridu za ku iya tabbatarwa.
Bugu da ƙari, yanzu haka ina da yara masu koyon ita wannnan sana’ar a masana’antar tawa.

Menene sirrin nasarar Yahya Dogon daji?

Hakuri, Jajircewa da kuma rike gaskiya, su ne sirrin samun nasarata a dukkan fannin rayuwarmu ta yau da kullum. Sanin kowa ne a nan Nijeriya akwai yawan ƙalubale masu yawa don haka sai an saka haƙuri da jajircewa.

Kasancewar Dogon daji sananne ne a kafafen sada zumunta na zamani, kuma mutane suna sane da irin gudummawoyin da kake bayarwa. Waɗanne nasarori za ka iya cewa ka samu a wannan sana’a taka da kuma abubuwa da kake yi na taimakon alumma?

Tabbas na samu nasarori masu yawan gaske da ba zan ma iya kawo ko rabin su a yanzu ba. Domin kuwa kafafen sada zumunta sun taimaka min sosai wurin samun bunƙasa da samun ɗimbin kwastomomi a dukkan faɗin Nijeriya da ma sauran ƙasashen Afirka ta yamma. Bayan wannan, na kasance ina amfani da kafafen sada zumunta domin taimakon al’umma musamman ma dai matasa. Domin na duƙufa sosai wurin samo wa matasa damarmaki na aiki da kuma guraben tallafin karatu a nan Najeriya da ma sauran manyan ƙasashen duniya bakiɗaya. Ina da tabbaci da yaƙinin cewa a wannan sashen na taimaki matasa fiye da 2000, tun daga lokacin da na fara wannan aiki na taimakon al’umma (Online Community Service).

Waɗanne ƙalubale kake fuskanta yanzu a sana’a da harkokinka?

Dukkan fannin na rayuwa to za a iya samun ƙalubale. Ni dai ɗan ƙalubalen da nake samu a tawa sana’ar da kuma aikin taimakon al’umma da nake bai wuce rashin samun taimako da kula ba daga gwamnati. Inda gwamnati za ta shigo cikin wannan lamari, to tabbas za a ƙara samun yawan dubban matasan da za su samu rayuwa mai kyau a nawa fannin. Domin wannan aikin zai ƙara bunƙasa sosai.

Kana ganin akwai wani lokaci da za ka iya barin sana’ar nan ka yi ritaya nan gaba?

Tabbas akwai, domin kuwa komai na rayuwa yana da adadi. Sai dai ko a yanzun nan na ajiye wannan sana’ar ba abunda zan ce sai dai na yi hamdala ga Allah Subhanahu wata’ala. Domin na tabbata nasarorin dana samu da kuma dubban matasan dana horar za su ci gaba daga inda na tsaya.

Wanne kira kake da shi ga matasa waɗanda suke ganin idan sun yi karatun boko mai zurfi sun fi ƙarfin ire-iren waɗannan sana’o’in hannun?

Ina ƙara kira da faɗakar da matasa domin su san cewa duk karamcin sana’a wallahi ta fi maula. Su yi qoqari su a je girman kai da kasala su tashi tsaye tsak su jajirce su nemi sana’a.

Meye saƙonka na ƙarshe?

Saƙo na na ƙarshe ko magana ta ta kashe ita ce, matasa nagari ke samar da al’umma tagari. Don haka, make kira ga iyaye, shuwagabanni da dukkan sauran al’umma gabaɗaya da su san cewa ya zama dole ga kowannenmu da ya tashi tsaye tsak domin ba da tashi gudummuwa domin tabbatar da samun al’umma tagari domin samun arziki da zaman lafiya mai ɗorewa a nan Nijeriya da ma duniya bakiɗaya.