Ƙwarin tubalin tattalin arzikin Sin yana ƙara wa kamfanonin waje ƙwarin gwiwar zuba jari

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Wani rahoton kafar yaɗa labarai ta china Daily ta ƙasar Sin, ya ruwaito a yau Talata cewa, kamfanonin ƙasashen waje na ƙara imani da tattalin arzikin kasar Sin kuma sun ƙarfafa ƙudirinsu na fadada zuba jari a ƙasar Sin.

Wannan baya rasa nasaba da ci gaban tattalin arziki da ƙasar ta samu cikin rabin farko na bana, inda ya ƙaru da kaso 2.5. Wannan kuma na da alaƙa da tubali mai kwari da aka gina tattalin arzikin ƙasar a kai.

Yayin da ake fama ɓullar annobar COVID-19 da wasu matsalolin duniya, haƙiƙa ƙasar Sin ta yi namijin ƙoƙari wajen tabbatar da tattalin arzkinta ya bunƙasa ta hanyar dabarunta na hangen nesa da kuma buɗe kofarta ga waje.

Ko a baya-bayan nan, babban bankin kasar ya sanar da ƙudurinsa na daukar wasu manufofin kuɗi domin taimakawa dukkan ɓangarorin tattalin arziki. Har kullum, ƙasar Sin bata ƙasa a gwiwa wajen samar da yanayi mai kyau na haɓakar tattalin arziki, ta hanyar taimakawa dukkan ɓangarori.

Duk da irin ɓata mata suna da ake yi, ƙarin kamfanonin waje na ƙara ƙarfafa imaninsu da ita, saboda sun amince da manufofinta, haka kuma ta na ƙoƙarin samar musu da yanayi mai kyau da ƙara haɓaka ɓangarorin zuba jari.

Yadda ƙasar Sin ke jagorantar ɓangaren fasahohin zamani, ya kara jan hankalin ‘yan kasuwar ƙasashen ketare. A kullum duniya na sauyawa, don haka, tafiya da zamani ya zama dole muddun ana son samun ci gaba.

Kuma ƙasar Sin ta samar da wannan yanayi inda take ƙarfafa gwiwar kirkire ƙirƙiren sabbin fasahohin zamani, ɓangaren da ya ƙara wa tattalin arzikin ƙasar da ma ‘yan kasuwa kuzarin zuba jari.

Haka zalika, yayin da a ko ina a duniya ake fama da hauhawar farashin kayayyaki fiye da kima, wannan lamari a ƙasar Sin yana kan wani matsakaicin mataki, inda babban bankin ƙasar ya yi imanin cewa, matakin zai daidaita.

A gaskiya dabarun ƙasar Sin suna haifar da da mai ido, domin suna tallafa wa al’ummar kasar da yan kasuwar kasashen ketare har ma da taimakwa bunƙasar tattalin arzikin ƙasashen dake haɗin gwiwa da ita da ma duniya baki ɗaya.