Daga HASSAN IMRAN
Matasa su ne jijiya da kuma makamin kowacce al’umma. Wannan ya sanya al’ummomin da suka gabace mu suka ɗau ƙwararan matakai wajen tarbiyyar matasansu da kuma cusa musu ruhin kishin addini da kyawawan ɗabi’u. Amma domin maƙiyanmu ba sa son mu da cigaba, suna kan bibiyar hanyoyi daban-daban da za su halaka matasanmu da kuma ɗabi’armu. ɗaya daga cikin munanan makamin da suke amfani da shi wajen yaƙar mu shine ta hanyar cusa sha’awar ta’amuli da miyagun ƙwayoyi a zukatan matasanmu. Daga cikin waɗannan ƙwayoyin akwai su kodin, totolin da ganyen Colorado.
Shi ganyen Colorado na ɗaya daga cikin miyagun ganyayyaki masu bugarwa ko kuwa cutar da wasu muhimman gaɓoɓi a jikin ɗan adam. Masana sun yi bayanin cewa daga cikin illolin ta, akwai janyo ciwon zuciya, da tayar da hawan jini, ciwon farfaɗiya, matsalar taɓin hankali da sauransu.
Abin takaici ne kuma abin haushi, yadda wannan ganyen Colorado ya zama ruwan dare a cikin al’umma. Matasa na shan ta kamar tabar sigari. Yanzu babu wata unguwa da za ka je ba za ka tarar da dandazon matasa a lunguna da kwangayen jama’a, suna shan ta ba. Daga cikin musabbabin wannan lalacewa akwai rashin kularwa iyaye wajen ba da kyakkyawar tarbiyya ga ‘yanyansu.
Rashin ilimin addini da na zamani shi ma ɗaya ne daga cikin abubuwan da ya ƙara rura wutar wannan taɓarɓarewar tarbiyya. Tasirin abokan banza akan wasu ‘ya’yanmu ya jefa da yawa a cikinsu a halaka.
A mako da ya wuce, jaridar Blueprint Manhaja ta wallafa labarin wani mutum da ya yi tsalle ya faɗa a cikin kogi sakamakon shan miyagun ƙwayoyi. Bincike ya nuna cewa daga cikin abubuwan da ke janyo tunanin mutum ya kashe kansa akwai shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da ke haifar da taɓin hankali.
Hanyoyin da za mu yaƙi wannan mugunyar halayya akwai buƙatar iyaye su ƙara sa ido matuƙa akan tarbiyyar ‘ya’yansu. Haka kuwa shugabanni su kawo tsarin da za a koyar da yara illolin shan miyagun ƙwayoyi a makarantu daga matsayin firamare har zuwa jami’a. Matasa su nemi aikin dogaro da kai su guji zaman kashe wando wadda ke haifar da munanan tunane-tunane da shan miyagun ƙwayoyi. Hukumar da ke da alhakin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi su yi iya ƙoƙarinsu wajen daƙile wannan halayya da kuma kama masu safararta. Muna kuma bai wa Gwamnatin Tarayya shawara kan ta ƙara ƙarfafa musu gwiwa da duk agajin da suke buƙata wajen daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a ƙasar nan. Gwamnatin ta ɗauki ƙwararan matakai wajen hukunta duk wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi da aka kama.
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga garin Jos, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa na yanar gizo kamar haka [email protected]