‘Ƴan bindiga sun kashe fararen hula sama da 35 a Gabashin Congo

Fararen hula fiye 35 ne wasu mayaƙan ƙungiyar CODECO suka kashe, a wani hari da suka kai wasu ƙauyuka da ke lardin Ituri na Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo a daren ranar Litinin.

Basaraken ƙauyen Djugu, Jean ɓianney ya ce ƴan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 8 na daren Litinin, inda suka kashe mutane tare kuma da ƙona gidaje.

Ya ce izuwa safiyar Talatar, sun gano gawarwaki sama da 35, bayaga waɗanda suka samu raunuka da kuma asarar dukiyar da aka tabka.

Shugaban wata ƙungiyar farar hula a yankin Jules Tsuba, ya ce izuwa safiyar Talata, sun gano gawarwakin da suka kai 49, kuma har yanzu ana ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.

Ita dai ƙungiyar CODECO na daga cikin ƴan bindigar da ke kai hare-hare a Gabashin Congo, inda a shekarun baya Majalisar ɗinkin Duniya ta zargeta da kai hare-hare kan makiyaya ƴan kabilar Hema, wanda ka iya sanya a tuhumi ƙungiyar da aika laifukan yaƙi da keta hakkin ɗan Adam.