Ƴan sanda sun ƙaddamar da binciken kisan tsohon janar a Abuja

Daga Buhari Aliyu Muhammad

Kwamishinan ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh, ya bayar da umurnin gudanar da binciken kisan da wasu da ake zargi ‘yan fashi ne suka yi wa wani tsohon Janar a gidansa da ke Abuja.

Maharan sun kutsa gidan marigayin – Burgediya Janar Uwem Udokwere mai ritaya inda suka kashe shi.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an kashe tsohon janar ɗin a gidansa da ke rukunin gidajen ‘Sunshine’ a unguwar Lokogoma da ke birnin tarayyar, ranar Asabar da tsakar dare.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma jajanta wa iyalan marigayin, tare da alƙawarta farauto waɗanda suka yi aika-aikar domin gurfanar da su a gaban shari’a.

”Za mu yi duk abin da ya kamata don tabbatar da kamo maharan domin gurfanar da su a gaban shari’a domin su girbi abin da suka shuka”, in ji sanarwar.