Wasu ‘ƴan bindiga dake zaune a yankin karamar hukumar Ukum ɗin jihar Benuwai sun fara amsar haraji daga ƙauyukan dake cikin ƙaramar hukumar.
Wani dan garin da ke bayani, yace yan bindigar sun fara ɗorawa gidaje harajin miliyan N20. Ya cigaba da bayani yana cewa, yanzu halin da ake ciki kowanne gida an yanke masa abinda zai rinka biya domin a samu a haɗa kuɗin harajin kafin watan ya ƙare.
Ya ƙara da cewa babu wanda ya isa a garin yanzu haka yayi jayayya ko kuma sanar da hukuma halin da ake ciki, saboda waɗannan ‘ƴan ta’addan sunyi karfi. Sunan shugaban ‘ƴan bindigar “Full fire”