Ɓangarori daban-daban a Amurka sun yi kira a rage sanyawa ƙasar Sin harajin kwastam

Daga CMG HAUSA

A kwanan nan, akwai ɓangarori daban-daban a ƙasar Amurka, da suka ƙara yin kira, da a rage buga harajin kwastam kan hajojin ƙasar Sin. Manazarta na ganin cewa, ci gaba da ƙara sanyawa ƙasar Sin haraji, zai haifar da tashin gwauron zabi na farashin kayayyakin yau da kullum, abun da zai kawo illa ga farfaɗowar tattalin arzikin Amurka.

Babban kwamitin kula da kasuwanci na Amurka da Sin ya fitar da sanarwa a kwanan baya, inda ya ce, ƙara sanya harajin kwastam kan hajojin da Amurka take shigarwa daga ƙasar Sin, zai sa masu sayayya da kamfanonin Amurka su biya harajin da ba na dole ba. A sabili da haka, idan aka soke ƙarin harajin, zai rage farashin kayayyakin yau da kullum, al’amarin da zai sauƙaƙa rayuwar al’ummar Amurka.

Babban mataimakin shugaba mai kula da manufofin ƙasa da ƙasa na ƙungiyar ‘yan kasuwar Amurka, John Murphy ya wallafa wani bayanin dake cewa, ƙaruwar tattalin arzikin Amurka na ƙara fuskantar matsi, ciki har da tsawwalar farashin kayayyaki, da matuƙar rashin ma’aikata da sauransu. Bayaninsa ya ce, rage harajin kwastam, ba daidaita mawuyacin halin da Amurkawa ke ciki kaɗai zai yi ba, wato hauhawar farashin kaya, har ma da inganta ƙwarewar masu ƙere-ƙere na ƙasar a fannin takara.

A nata ɓangaren kuma, sakatariyar baitulmalin Amurka, Janet L. Yellen ta bayyana cewa, a halin yanzu gwamnatin kasarta na nazarin manufofin kasuwancinta kan ƙasar Sin, kuma soke harajin da aka ƙara sanyawa hajojn Sin, abun lura ne.

Binciken jin ra’ayin al’umma ya nuna cewa, sakamakon hauhawar farashin makamashi da kayan abinci da na sauran kayan masarufi, al’ummar Amurka na kara nuna rashin jin daɗi da gwamnatin Biden, al’amarin da ya sa ‘yan jam’iyyar Democrat ke fuskantar rashin kujeru masu rinjaye a yayin zaɓen ‘yan majalisar dokokin ƙasar, da za’a gudanar a watan Nuwambar bana.

Fassarawa: Murtala Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *