Ɓarayi sun dira gidan Jarumi Saka tare da buƙatar miliyan 20

Daga AISHA ASAS

Ɓarayi ɗauke da makamai sun afka wa gidan fitaccen jarumi barkwanci a masana’antar finafinai ta Kudu, wato Nollywood, Hafiz Oyetoro, wanda aka fi sani da Saka.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata, a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun.

Kamar yadda makusanci kuma abokin jarumin Kayode Soaga ya bayyana wa manema labarai, ɓarayin sun dira gidan Saka suna masu neman ya ba su zunzurutun kuɗi har miliyan 20, ko kuma su aika shi lahira.

“Ɓarayin sun shigo ne wuraren ƙarfe biyu na dare, ɗauke da manyan bindigogi taƙil da alburusai da kuma wasu makamai. Ba ɓata lokaci suka karya garkuwar gidan,” inji Kayode Soaga.

Ya ƙara da cewa, “sun fasa ƙofar ƙarfen gidan, sannan suka isa gare shi, suna masu umurtar sa da ya ba su miliyan 20 ko kuma su kashe shi.

Kuma sun shiga gidaje uku bayan na Hafiz, sannan sun yi ɓarna fiye da wadda suka yi a gidansa.”

Dangane da yadda ta kaya tsakanin varayin da jarumin da kuma yadda suka bar gidan, Kayode ya ce, “Saka ya dinga roƙo da neman alfarma kan ba shi da miliyan 20, sannan suka sauko da kuɗin zuwa miliyan uku. Nan ma ya sanar da su ba shi da su.”

Ya kuma ƙara da cewa, “sun azabtar da shi matuƙa kafin su kwashe duk wayoyinsu ƙirar ‘Android’ da kuma komfutoci qirar apple tare kuma da duk kuɗin da ke gidan.

Baya ga haka sun kwashe dukka katin cire kuɗi (ATM) inda suka yaye abinda yake asusun ajiyar su ta hanyar amfani da POS da suka zo da shi.”

“Mun gode Ubangiji da ya kuvutar da rayuwarshi. Yanzu haka yana nan cikin ƙoshin lafiya,” Kayode ya ƙara faɗa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *