Ɓata-gari sun cinna wa ɓangaren ƙabilar Ibo a kasuwar Legas wuta

Daga AMINA YUSUF ALI

Ana zargin wasu ɓata-gari da cinna wuta wacce har ta yi sanadiyyar tayar da gobara a kasuwar Legas ta sayar da kayayyakin gyaran mota wacce mafi akasarin ahalinta inyamurai ne, wato ‘yan ƙabilar Ibo.

Wannan kasuwar sayar da kayan gyaran mota tana kan titin Kirikiri, Ajegunle, ƙaramar hukumar Ajeromi ifelodun ta jihar Legas. Al’amarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba, 8 ga Maris, 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan hari da aka kai kasuwar sayar da kayan mota wacce akasarinta ƙabilar Ibo ne suke da rinjaye a cikinta an yi shi ne da gayya kuma aiki ne na zalunci wanda ake zargin wasu ‘yan daba sun yi tare da tallafin wasu ‘yan siyasa.

Hakazalika rahotanni sun bayyana cewa, an kashe maigadi a sakamakon harin da aka kai.

A halin yanzu dai ana binciken yadda za a gano waɗannan ɓata-gari da suka gudanar da wannan ɗanyen aiki don tabbatar da an miƙa su ga jami’an tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *