Ɓatan Naira tiriliyan biyar: Majalisa ta fara binciken hukumomi 252

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamitin Kula da Asusun Buƙatu na Majalisar Dokokin Tarayya, ya fara binciken kashe Naira tiriliyan 5 da Hukumomi 252 suka yi tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021.

Binciken na zuwa ne bayan gano hukumomi da dama na karɓar kuɗaɗe daga Asusun ba tare da sahalewar kwamitin da doka ta ba wa damar sa ido a kai ba da Majalisar Dattawan ta yi.

Shugaban Kwamitin, Sanata Mathewa Urhoghide ya ce, “muna so mu ga yadda aka kashe waɗannan kuɗaɗen ne, saboda akwai ruɗani akan tsarin fitar da kuɗin.

Ya kuma ce, Majalisar za ta aika da sammacin tiso keyar duk wata Hukumar da ta ki amsa kiran gayyatar kwamitin.

Kazalika, Sanatan ya ce Shirin Ci gaba Mai Ɗorewa na Gwamnati (SDG) ya samu Naira biliyan 180, sai NBET da ya karvi Naira Biliyan 2.9, yayin da ma’aikatar jin kai ta karɓi Naira biliyan 445.

Sauran Hukumomin da za su bayyana gaban kwamitin sun haɗa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu, da ta Tsaro, da ta Shirin Inshorar Lafiya na Gwamnati, da rundunar ’Yan Sanda, da Ma’aikatar Kula da Lantarki ta ƙasa.

Sauran sun haɗa da Bankin Ma’aikata, da Ma’aikatar Ba da ruwan sha, da Majalisar Tarayya, da Hukumar Yaƙi da Cin hancin da Karɓar ƙorafe-ƙorafe ta ƙasa haɗi da Hukumar Tsaro ta DSS.