Ɓatanci: Ganduje ya samu damar rataye Abduljabbar Kabara

*A gaggauta kashe ni, inji malamin
*Yadda kotu ta yanke masa hukuncin kisa
*An haramta karantawa ko sauraron wa’azinsa

Daga BABANGIDA S GORA a Kano

A ranar Alhamis ta jiya ne wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ta ke Ƙofar Kudu a cikin birnin Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta bai wa Gamnan Jihar Kano izinin kashe Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ta hanyar rataya, wanda ta samu da hannu dumu-dumu kan furta kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW) bayan kimanin shekara ɗaya da watanni biyar da gurfanar da shi a gabanta.

Malam Abduljabbar, wanda kotun ta same shi da laifuffuka guda huɗu, na farkonsu shine kan batun auratayyar Manzo Allah (SAW) da matarsa Nana Safiyya a cikin hadisi mai lamba 1,365 da hadisi mai lamba 1,428.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya karanta wa kotun cewa, malamin ya aikata laifin ɓatanci ne da ya saɓa wa kundin doka ta shari’ar Jihar Kano a sassa na 375 da 382.

Haka kuma wannan kalaman ɓatancin an yi rikodin ɗinsu ne a lokacin tare da sa shi a kafar sadarwa ta zamani da ya fi yawo a wani shafi mai suna Asahabul Kafi, yayin da Mai Sharia Sarki Yola ya buƙaci mai gabatar da ƙarar ya gabatar da shaidun da suka tabbatar da faruwar lamarin lokacin da abun ya faru.

Yayin gatabar da shaidun, mai gabatar da ƙarar ya gabatar da farfesa Ahmed Murtala da Adamu Adamu Gwale da Sufeto Muhammad Kabir tare da Kabir Muhammad matsayin shaidunsa.

Sannan mai gabatar da ƙarar ya tabbatar wa da kotun cewa, kalaman da malamin ya faɗa sun yi muni kuma ba sa bisa koyarwar sahihin malamanin hadisin manzon Allah (SAW) da mazhabar Imamu Malik, Allah ya yi masa rahama.

Alƙalin ya bayyana cewa, wanda ake tuhumar ya kasa kare kansa bisa laifin da ake tuhumar sa ya aikata, amma duk da haka kotun ta ƙara ba shi isashen lokaci, don ya kawo wata hujja mai ƙarfi da za ta kare shi, amma ya kasa gabatar mata da wannan hujja.

Kazalika, daga cikin tuhumar da ake masa, har da zargin wa’azinsa zai iya tayar da tarzoma a Jihar Kano.

Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya ɗage zaman kotun, don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin. Bayan ɗan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.

Sai dai kafin a tafi hutun, kotun ta bai wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara dama, don ya yi magana ta ƙarshe, inda ya ce, lauyan da ke kare shi bai san shi ba kuma ba ya neman afuwa, saboda a cewarsa bai aikata laifi ba, don haka a gaggauta yanke masa hukunci.

”Ni ba na neman sassauci akan wannan laifi da ban yi ba, Ina kuma bai wa almajiraina haƙuri, kar su samu damuwa kan tafiyata lahira, zan yi mutuwa ta girma, kuma ba na neman kai Ibrahim Sarki ka yi mun sassauci, kuma a gaggauta yi min hukuncin nan.” Kalamai na na ƙarshe kenan da Abduljabbar ya faɗa a kotun.

Bayan kotun ta sake zama, a yayin yanke hukuncin, mai shari’ar ya ce, kamar yadda kundin dokar shari’ar Jihar Kano, wanda aka tabbatar a shekara ta 2000 a sashe na 382 da 375 cewa, duk wanda ya furta wasu kalaman ɓatanci ga Manzon Allah (SAW), to hukuncinsa kisa ne.

Daga nan sai Alƙali Yola ya ce, “ni Ibrahim Sarki Yola, alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba ta ɗaya dake cikin Birnin Kano, kamar yadda na same ka da aikata laifi dumu-dumu na ɓatanci kuma da ya saɓa wa kudin dokar shari’ar Musulunci ta Jihar Kano da aka tabbatar a shekara ta 2000 kuma ya saba wa kundin dokar sashe na 283 (B) na shashen shari’a, na yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya.”

Sarki Yola ya kuma haramta amfani da dukkan masallatan malamin guda biyu dake Filin Mushe da kuma Sharaɗa a cikin Birnin Kano, sannan ya kuma umarci a mayar da littattafan guda 189 da malamin ya gabatar wa kotuna yayin zaman shari’a zuwa ɗakin karatu mallakar gwamnati Kano tare da hana sauraron dukkan wasu karatunsa a ko’ina.

Bayan yanke hukuncin, alƙali, cikin gaggauwa, ya buqaci idan malamin na da wata magana ya yi, yayin da malamin ya buƙaci mabiyansa da su kwantar da hankalinsu, yana fatan cikawa da imani tare da buƙatar zartar da hukuncin kotun cikin gaggawa na kisa akansa.

Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a, 16 ga Yuli, 2021, ne Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa tun bayan da gwamnatin Kano ta shirya wata muqabala tsakanin malaman Kano da shi malamin.

Sai dai ko a wancan lolacin, Shehin malami Abduljabbar Nasiru Kabara wanda shi ne mai kare kansa daga malamai huɗu: Malam Mas’ud Hotoro daga ɓangaren Ɗariƙar Ƙadiriyya kuma tsohon ɗalibin Sheikh Abduljabbar; Malam Abubakar Mai Madatai daga ɓangaren Tijjaniyya; Malam Kabir Bashir Ƙofar Wambai daga vangaren ƙungiyar Izala da kuma Dr. Muhammad Rabiu Umar Rijiyar Lemo daga ɓangaren Salafiyya, da ke zarginsa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, ya ce ba zai tuba ba a wurin wannan muƙabala, “saboda rashin ƙwararan hujjoji”.

Ya faɗi hakan ne a daidai lokacin da Malam Abubakar Madatai ya ce duk wanda ya ci mutuncin Annabi hukuncinsa kisa ne, sannan ya nemi Abduljabbar da ya fito fili ya tuba.

Sai malamin ya ce: “Ba zan tuba a wurin wannan muƙabala ba har sai an ba ni cikakkiyar hujja. Indai aka ba ni hujjojin da suka fi nawa zan tuba, amma yanzu mutum ba zai tuba ba bayan yana kan gaskiya. Ba a biyo turbar da zan tuba ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *