Ɓatanci: Kotu ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa

Daga WAKILINMU

Kotun Shari’a a Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotu ta yanke wa malamin hukuncin kisa ne bayan da ta same shi da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Da yake yanke hukuncin, Alƙalin Kotun ya kuma buƙaci Gwamnatin Kano ta ƙwace masallatai guda biyun da ke ƙarƙashin kulawar Abduljabbar.

Kazalika, Alƙalin ya yi kira da a daina sanya karatuttukan Abduljabbar ɗin a ɗaukacin kafafen yaɗa labarai, haka ma hotunansa.

Bayan haka, kotun ta bai wa malamin wa’adin kwana 30 a kan ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke masa ko kuma ya rasa damar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *