Ɓatanci: Sufin Zamani ya aika wa MOPPAN da takardar ban-haƙuri

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani ɓangare na cika sharuɗɗan da aka gindaya masa, mawaƙi Sarfilu Umar, wanda aka fi sani da Sufin Zamani, ya aika wa ƙungiyar shirya finafinai ta MOPPAN takardar ban-haƙuri.

Hukumar DSS ce ta buƙaci mawaƙin ya rubuta takardar ban-haƙurin bayan da ta kama shi da laifin yi wa matan Kannywood ɓatanci cikin wata waƙa da ya yi.

A cikin takardar da ya rubuta, Sufin Zamani ya jaddada nadamarsa ta yin waƙar ɓatancin, tare da bada haƙuri yadda ya kamata.

Cikin sanarwar da Kakakin MOPPAN na Ƙasa, Al-Amin Ciroma ya fitar ta nuna cewa, wannan tabbaci ne kan cewa mawaƙin ya ɗauki dukkanin gyaran da aka yi masa.

Manhaja ta ruwaito yadda MOPPAN ta gurfanar da Sufin Zamani a gaban hukumar DSS bayan da matan masana’antar Kannywood suka gabatar wa MOPPAN ƙorafinsu kan ɓatancin da mawaƙin ya yi musu a wata waƙarsa da ya shirya.

Bayan da ta gudanar da bincikenta kan batun, DSS ta damƙe Sufin Zamani kana daga bisani ta ba da belinsa bisa wasu sharuɗɗa, ciki har da rubuta wa MOPPAN da takardar ban-haƙuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *