Ɗakin otel ɗin da ake biyan sama da Naira miliyan 22 a kwana ɗaya

A halin da ake ciki yanzu, an wallafa bidiyon wani otel da ke ƙarƙashin ruwa wanda ya jawo muhawara a shafukan sada zumunta na zamani.

Shi dai wannan otel shi ne babban otel na farko a ƙarƙashin ruwa a duniya.

An ruwaito cewa, ana biyan Shiling miliyan 5.5 na ƙasar Kenya (kimanin Naira miliyan 22) duk ɗaki guda da ke otal ɗin a kowane dare.

Babban otal ɗin Muraka na ƙarƙashin ruwa shi ne irinsa na farko a duniya kuma ya ƙunshi wani yanki na tsibirin Maldibes Rangali Island Resort wanda ke cikin ƙasar Maldibes ta Kudancin nahiyar Asiya.

Conrad Maldibes ne ya yaɗa bidiyon a lafar Instagram tare da ɗaukar ɗaya daga cikin manyan ɗakunan kwana na otal ɗin da ke ƙarƙashin teku mai nisan ƙafa 16 a Tekun Indiya.

A wannan gini mai ban sha’awa akwai wurin wanka mai zaman kansa. Ɗaya daga cikin manyan ɗakunan yana ɗauke da banɗaki da kuma ɗakin barci.

Kimanin masu ziyara 360 na iya zuwa don kallon tekun Indiya. Wata da ta kalli bidiyon ta yi sharhi, inda ta ce, “menene manufar ziyartar otel ɗin. Idan ni da abokin zamana mun ziyarci otal ɗin, me zai sauya mu? Tunanin wannan wuri kaɗai zai iya sanya zuciya ta karaya.”

Wata kuwa mai ta ce, “ba da ni ba, ba zan taɓa tunanin wani zai kai ni wannan wuri domin ya burge ni ba. Don haka, ba abin gwaninta ba ne a wurina.”