Ɗaliba ta ciji lakcara bayan rikici ya ɓarke a yayin ɗaukar bidiyon TikTok

Daga BELLO A. BABAJI

Wani al’amari na ban mamaki ya auku a tsangayar nazarin wasan kwaikwayo da dangoginsa ta Jami’ar Nnamdi Azikwe (UNIZIK) yayin da aka samu wata ɗaliba ta farmaki wani malami tare da gantsara masa cizo.

A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen labarai, an ga yadda ɗalibar ke tiƙar rawa a wani babban ɗakin karatu da nufin ɗora shi a manhajar TikTok.

A yayin haka ne wani malami ya zo wucewa inda ya taɓa bayanta da nufin yi mata alamar ta dakta da ɗaukar.

Wasu rahotanni daga baya sun nuna cewa malamin ya buƙaci ɗalibar da ta goge bidiyon da aka ɗauka kasancewar fuskarsa ta bayyana aciki.

Lamarin da ya haifar da ja’inja da rikici a tsakaninsu wanda hakan ya kai ga zargin ɗalibar da cizon malamin sau waɗansu adadi.

Shaidu sun ce, a lokacin da malamin ya ke ƙoƙarin dakatar da ita ta hanyar riƙe hannayenta ne sai ta ƙara fusata, inda ta yaga masa tufafi da tsinke shi da mari gami da kartar fuskarsa.

A yayin tabbatar da faruwar al’amarin, Shugaban jami’an tsaron jami’ar, Ken Chukwurah ya ce makarantar ta fara gudanar da bincike game da haƙiƙanin abinda ya faru.