Ɗaliban Greenfield 14 sun samu ‘yanci

An sako ɗalibai 14 na Jami’ar Greenfield ta Jihar Kaduna da ’yan bindiga suka sace daga ɗakunansu na kwana tun a watan Afrilun da ya gabata.

Bayanai sun nuna an sako aɗaliban ne a ranar Asabar bayan biyan kuɗin fansar da ba a fayyace ba.

Mai Magana da yawun jami’ar, Kator Yengeh, ya tabbatar wa manema labarai da batun sako ɗaliban, tare da cewa nan gaba kaɗan Hukumar Gudanarwar Jami’ar za ta yi ƙarin haske kan lamarin.