Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗaruruwan ɗaliban Jami’ar Tarayya Gusau da ke Jihar Zamfara sun tare hanyar Gusau zuwa Kaduna domin nuna rashin jin daɗinsu game da sace ɗaliban jami’ar su biyar.
A daren Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace ɗaliban makarantar lamarin da ya harzuƙa ɗaliban da suka rufe hanyar, wanda hakan ya sa masu ababen hawa da dama suka maƙale na tsawon sa’o’i.
Ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi na tarwatsa ɗaliban ya ci tura, inda da yawa daga cikinsu ke zaune a kan babbar hanyar, inda suka yi kira ga hukumomin da suka dace da su ɗauki matakin gaggawa kan matsalar tsaro a jami’ar.
Mataimakin Shugaban jami’ar, Farfesa Muazu Abubakar, wanda ya kasance a wurin da lamarin ya faru ya yi kira ga ɗaliban da suka yi zanga-zangar da su bar masu ababen hawa su yi zirga-zirgarsu a hanyar amma suka ƙi sauraron roƙonsa.
Farfesa Muazu ya tabbatar wa ɗaliban cewa hukumar jami’ar za ta yi ƙoƙarin ganin an samar da ingantaccen tsaro a makarantar, amma ɗaliban sun dage cewa ba za su je ƙo’ina ba.
Yayin haɗa wannan rahoto ɗaruruwan motoci ne suka cika titin, yayin da ɗaliban suka ci gaba da ihu suna cewa gwamnatocin sun gaza.
Ɗaya daga cikin ɗaliban Musa Shehu wanda ya zanta da jaridar PUNCH ya bayyana cewa an yi garkuwa da ɗalibai da dama a baya amma ba a ɗauki matakin ceto su ba.
Ya ce, “An sace ɗalibai da yawa daga wannan makarantar amma ba a ɗauki wani sahihin matakin ceto su ba.
“Akwai wasu ɗalibai a halin yanzu a sansanin ‘yan bindiga, kuma hukumomi ba su yi wani yunƙuri na ceto su ba,” in ji ɗalibin.