
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu ɗaliban makarantar Ebira Muslim Community College Okengwe (EMCCO) dake ƙaramar hukumar Okene a Jihar Kogi, sun farmaki wani malami mai suna Mista Muktar Salihu inda suka lakaɗa masa dukan kawo-wuƙa da ya kai ga an kai shi asibiti tare da kwantar da shi a ɗakin jinya na musamman.
Ana zargin cewa ɗaliban ƴan ƙungiyar asiri ne kuma ƴan aji biyu a babbar sekandire.
Lamarin, wanda ya haifar da damuwa acikin al’umma, ya faru ne a ƙoƙarin shirin ƙungiyar na mamaye kwalejin.
Jaridar PeoplesPen ta ruwaito cewa an yi zargin wani mai suna Abdulbatin, wanda ɗa ne ga wani sarkin gargajiya na Masarautar Esusu da ke gundumar Okengwe a ƙaramar hukumar, shi ne shugaban ƙungiyar.
Majiya da dama sun bayyana cewa, Mista Salihu malami ne da ke koyar da darasin Physics wanda bayan ɗaliban sun casa shi ne, sai aka garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
Wani malami da ya buƙaci a sakaye sunansa ya yi kira ga hukumomi da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace don kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.
Tuni rundunar ƴan sandan yankin ta umarci Sarkin Esusu da ya tabbatar da cewa ɗansa ya halarci ofishinta don amsa tambayoyi.