Wani ɗalibin makarantar sakandaren Obada Idi-Emi da ke ƙaramar hukumar Imeko Afon a jihar Ogun, mai suna Ariyo, ya mutu bayan da wani malami ya lakaɗa masa duka har bulala 24 da kuma tsallen kwaɗi 162 saboda fasa kwandon shara.
Wani mai fafutuka mai suna Adetoun ya bayyana lamarin a shafinsa na Instagram a ranar Juma’a.
A cewar Adetoun, malamin ya kawo kwandon shara zuwa ajin Ariyo tare da umarnin kada ɗaliban su fasa kwandon sharar.
Ta bayyana cewa Ariyo cikin zolaya ya amsa wa malamin cewa an sayo kwandon shara ne da kuɗin ɗaliban, matakin da aka ce ya harzuƙa malamin.
An ce malamin ya kai rahoto ga shugaban makarantar wanda ya ba da umarnin a hukunta ɗalibin.
A bisa umarnin shugaban makarantar, malamin ya yi wa Ariyo bulala 162 da sanda kuma ana cikin haka ne ɗalibin ya yanke jikinya faɗi.
Adetoun ya ci gaba da cewa malamin da wasu ma’aikatan makarantar da ke wurin sun yi jinkiri wajen kai Ariyo asibiti domin kula da lafiyarsa, kuma bayab da suka kai shi sainya ce ga garin ku nan.
Wani babban jami’in ‘yan sanda ya tabbatar da labarin faruwar lamarin, amma ya ce ba a ba shi izinin yin magana da manema labarai ba.
Ya ce lamarin ya haifar da tashin hankali a yankin amma shiga tsakani da ‘yan sanda suka yi ya sa aka shawo kan lamarin.
“Muna kan lamarin, lamarin ya so haifar da tashin hankali amma mun sami nasarar kawar da tashin hankalin,” inji majiyar ‘yan sandan.
Da take tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta ce an tabbatar da mutuwar ɗalibin a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Abeokuta, babban birnin jihar.
Ta ce, “Lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Oktoba, 2024. An buƙaci marigayin ya yi tsallen kwaɗi 162, kuma an yi masa bulala 24 sa sanda.