Ɗan ƙwallo ya rasu ana tsaka da wasa

Daga BELLO A. BABAJI

Wani ɗan wasan ƙwallon ƙafa mai suna Adeyemi Adewale mai shekaru 29 da ke ƙungiyar Ilesa ta Yamma ya rasa ransa a lokacin da ake tsaka da buga wasa a Jihar Osun.

Adewale ya yanke jiki ne a lokacin suke buga wasan ƙarshe na kofin tunawa da Adeleke a Makarantar Ataoja ta Kimiyya.

Daga nan ne aka garzaya da shi Asibitin koyarwa na Jami’ar Osun inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Kakakin ƴan sandan jihar, Yemisi Opalola ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya na mai cewa tuni suka fara bincike game da lamarin.

Tuni aka garzaya da gawar mamacin wajen ajiyar gawa dake asibitin.