Daga USMAN KAROFI
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Basira FC da ke Lafia ta tabbatar da rasuwar ɗan wasanta, Promise Andrew, bayan tiyata da aka yi masa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, Ƙungiyar ta ce:
“Ƙungiyar Basira FC ta na cikin alhinin rasuwar ɗan wasanta, Promise Andrew, wanda ya rasu a ranar Juma’a, 7 ga watan Fabrairu, 2025, bayan tiyata da aka yi masa a Lafia.
“Marigayi Promise ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan wasan da suka halarci tantancewar Ƙungiyar don kakar wasanni ta 2024/2025, kuma ya shafe sama da watanni shida yana taka leda a Ƙungiyar.
“Mu na cike da jimami, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokansa, da ɗaukacin al’ummar ƙwallon kafa. Za a tuna da kyakkyawar alaƙar da ya yi da sauran ‘yan wasa da shugabannin ƙungiyar. Muna addu’a Allah ya jiƙansa da rahama. Amin.”