Ɗan banga ya harbe mahaifinsa yayin gwada maganin bindiga

Wani ɗan banga ya baƙunci lahira a yayin da yake gwada maganin bindiga a Jihar Adamawa.

Magidancin da ya sha maganin bindiga ya ɗora bindigarsa ce a cikinsa sannan ya tursasa wa ɗansa mai shekara 19 ya harba ta.

Harba bindigar da ɗan ya yi ke da wuya ta tashi da mahaifin, ta kuma yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis a Ƙaramar Hukumar Jada ta jihar.

Jami’in ya ce, su na gudanar da bincike kuma duk wanda ke da hannu a cikin lamarin zai fuskanci hukunci.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji amfani da makamai, waɗanda ke da izinin mallakar su kuma su tabbata sun kiyaye ƙa’idoijin kariyar rayuwarsu da ta wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *