Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A ranar Alhamis ne aka naɗa Muhammad Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan Jihar Kaduna da kuma ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, Erhiatake Ibori-Suenu, a matsayin shugabannin kwamitoci na dindindin.
Kakakin Majalisar Abbas Tajuddeen ne ya sanar da kwamitoci 134 na dindindin a zaman majalisar.
Yayin da aka naɗa ɗiyar Ibori a matsayin shugabar kwamitin majalisar wakilai na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), an bayyana ɗan El-Rufai a matsayin shugaban majalisar dokokin banki.
Tsohon mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Idris Wase, tsohon shugaban majalisar, Alhassan Ado Doguwa, Yusuf Adamu Gagdi, Mukhtar Betara suma sun zama shugabannin kwamitoci.
Ikenga Ugochinyere ya zama shugaban albarkatun man fetur (Downstream) yayin da Alhassan Ado Doguwa ya zama shugaban albarkatun man fetur (Upstream).
Kabir Alhassan Rurum ya zama shugaban kwamitin harkokin sufurin jiragen sama na majalisar, yayin da Abdulmumini Jibrin ya samu shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ƙasashen waje.
Abubakar Kabir Abubakar Bichi, wanda shine shugaban kwamitin ayyuka a majalisar ta tara, yanzu shi ne shugaban kasafin kuɗi.
Betara wanda ya jagoranci kwamitin kasafin kuɗi a majalisar wakilai ta 9 a yanzu shine ya jagoranci kwamitin majalisar kan babban birnin tarayya (FCT).
Yusuf Adamu Gagdi ya cigaba da riqe shugabancin kwamitin majalisar kan sojojin ruwa tare da Leke Abejide wanda shi ma ya riƙe kwamitin sa na hukumar kwastam ta majalisar.