Ɗan gidan El-Rufai na yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Kaduna barazana kan binciken da ake yi wa mahaifinsa

Daga BASHIR ISAH

Kakakin Majalisar Jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya zargi ɗan gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai, kan tura masa rubutaccen saƙo yana yi masa baraza kan batun binciken tsohuwar gwamnatin mahaifinsa.

MANHAJA ta kalato a ranar Talatar da ta bagabata Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin na musamman domin bincikar hada-hadar ƙuɗaɗe da kwangiloli da sauransu, wanda tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi daga 2015 zuwa 2023.

Kakain Majalisar ya gargaɗi Bello kan ya daina yi wa majalisar barazana kan batun bibciken.

Liman ya ƙara da cewa, Bello ya aike masa da saƙon zagi da barazana ta manhajar WhatsApp game da binciken da majalisar take gudanarwa a kan mahaifinsa.

Kazalika, Kakakin ya zargi Bello da wallafa saƙonni masu nuni da “faɗa”, sannan ya nuna rashin maratabawa ga mamabobin Majalisar Dokokin Jihar.

Bello El-Rufai shi ne ɗan majalisa mai wakiltar Mazaɓar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Tarayya.