Ɗan jairida ya zo na biyu a gasar rubutattun waƙoƙin Hausa a Sakkwato

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Ɗan jarida Bashir Yahuza Malumfashi ya samu nasarar zama na biyu a gasar rubutattun waƙoƙin Hausa da aka gudanar a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato.

Bashir ya wallafa bayanin nasarar tasa ce a shafinsa na facebook da yammacin Laraba inda ya nuna farin cikinsa dangane da nasarar da ya samu.

Ya ce, “A yau Laraba, 04-12-1442 (Hijriyya) daidai da 14-07-2021 (Miladiyya) aka gudanar da bikin Gasar Rubutattun Waƙoƙin Hausa da Sashin Hausa na Jami’ar Usman ‘Danfodiyo Sakkwato ya shirya.

“Allah da ikonSa na shiga gasar rubuta waƙa ta Gani-Ga-Ka, inda mu 42 muka fafata, muka rubuta baitoci 10 cikin minti 20 a kan Zaman Lafiya. NI ne na zo na biyu, na doke ‘yan takara 40.

“Alhamdu lillahi, an karrama mu a gaban jama’a, inda Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya miƙa mani satifiket da tukwici na musamman.”

Hotunan bikin da Bashir wallafa a shafinsa na facebook sun nuna yadda ya karɓi kyautarsa da kuma yanayin mahalarta taron gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *